Wata kotun al’ada dake zamanta a yankin Mapo na Ibadan a jihar Oyo ta amince da bukatar wata mata, Crolyn Adetoro ta neman a raba aurenta da mijinta bayan ya yi watsi da ita saboda ya kara aure.
Carolyn, wacce ’yar kasuwa ce kuma mazauniyar unguwar Felele ta Ibadan dai ta shafe shekaru 21 tana auren mijin nata mai suna Adeleke kafin bukatar raba auren ta taso.
- Kotu ta ki amincewa da bukatar kwace kadarorin Saraki
- Abin da ya sa har yanzu ba mu biya ma’aikatan zaben Kano hakkokinsu ba – KANSIEC
Da yake yanke hukunci, Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade ya ce kotun ta amince da bukatar ne saboda dukkan ma’auratan biyu sun amince da bukatar hakan.
Mai Shari’ar ya kuma ba mijin damar ci gaba da kula manyan ’ya’yansu su uku, sai kuma matar za ta kula da kananan ’ya’yan guda biyu.
Ya kuma umarci mijin ya rika biyan N5,000 a kowanne wata domin kula da yaran.
Yayin da take bayar da shaida a gaban kotun, Crolyn ta ce, “Tun da mijina ya kara aure kullum sai ya lakada min dukan tsiya. Da alama yanzu ba ya kaunata ko kadan.
“Yana zargina da cewa ni na jefa shi cikin halin da yake ciki yanzu. Ina bukatar kotun nan da ta bani damar ci gaba da kula ‘ya’yanmu guda hudu saboda dama nice nake kula da su tsawon wannan lokacin,” inji matar.
Da yake mayar da martani, Adeleke ya amince da bukatar raba auren da matar tasa.
“Ta yanke shawarar kawo ni kara ne saboda na shawarceta da ta daina rigima da mahaifiyarta wacce take bata shawara ta gari amma take kunnen kashi da ita.
“Matar nan ta kan ci amanata. Na taba kamata dumu-dumu tana mu’amala da maza,” inji Adeleke.