Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Mai shari’a Nnamdi Dimgba ya ce umarnin wucin-gadi na a kwace wasu kadarori da aka gano na Gwamnan Jihar Ekiti Mista Ayo Fayose ne bai saba wa Sashi na 308 na Tsarin Mulkin Najeriya ba.
Alkalin ya ce, ba manufar rigar-kariya da aka ba wadansu masu rike da mukaman gwamnati ba ce ta hana hukumomin tsaro bincikarsu domin samun shaidun da za a yi amfani da su a nan gaba.
Mai shari’a Dimgba ya yanke wannan hukunci ne a ranar Talatar da ta gabata sakamakon wata bukata ta Gwamna Fayose, inda lauyansa Mike Ozekhome (SAN), ya nemi kotun ta janye umarnin wucin-gadi da ta ba Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) a ranar 20 ga Yuli.
Umarnin dai yana da alaka da binciken da Hukumar EFCC ke yi ne kan wasu aikace-aikace na Gwamnan da wadansu mukarrabai da makusantansa.
Kadarorin da lamarin ya shafa sun hada da wasu gidaje hudu masu dakunan kwana hurhudu da suke jere masu lamba 3 da 4 da 6 da 9a fuloti na 100 da ke Tiaminu Sabage, a Tsibirin bictoria Island, a Jihar Legas.
Sai kuma wanda yake lamba 44 Osun Crescent, Maitama, Abuja da fuloti na 1504, Yedzeram Street, Maitama Abuja.
Hukumar EFCC a bukatar da ta gabatar a gaban kotun ta cika takardar rantsuwa cewa an sayi kadarorin ne da kudin almundahana, inda ta yi zargin Gwamna Fayose ya saye su ne da kudin cin hanci da ya samu daga ’yan kwangila da sauran ayyukan rashawa.
Kuma ta ce wasu daga cikin kudin da aka sayi kadarorin sun fito ne daga cikin Naira biliyan 1 da miliyan 219 da dubu 940 da wani bangare ne na Naira biliyan 4 da miliyan 745 da aka sace daga baitul malin Gwamnatin Tarayya ta amfani da ofsihin tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro.
A ranar 21 ga Yuli, Ozekhome ya bukaci kotun ta jingine umarnin bisa hujjoji 10 da ya gabatar ciki har da rashin hurumi ga kotun na saurare da bayar da umarnin da kuma batun rigar-kariya da Gwamnan yake da ita a karkashin Sashi na 308. Sai dai Mai shari’a Dimgba ya amince da hujjar lauyan EFCC, Andrew Akoja, ta cewa umarnin na 20 ga Yuli ya dace.
Mai shari’a Dimgba ya ce duk da Sashi na 308 na Tsarin Mulki ya ba gwamnoni kariya daga jelen zuwa kotu domin ba su damar gudanar da mulkin jama’a, to amma bai kamata a fassara hakan ta hanyar da za a murkushe yaki da cin hanci ba, ta yadda hakan zai nuna cewa Hukumar EFCC da sauran hukumomin bincike ba za su iya sanya ido kan dukiya da kadarori ko asusun wani Gwamna mai ci ba, domin sanya ido da samun shaidun da za su yi amfani da su a nan gaba ba, don haka sai ya yi watsi da bukatar.
Kotu ta amince a kwace wasu kadarorin Gwamna Fayose
Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Mai shari’a Nnamdi Dimgba ya ce umarnin wucin-gadi na a kwace wasu kadarori da aka gano na Gwamnan…