Mai Shari’a Efe Ikponmwonba na Babbar Kotun Jihar Edo, ta yanke wa wasu ’yan damfarar intanet hudu hukuncin dauri a gidan yari, bisa samun su da laifin zamba cikin aminci.
Jami’an Hukumar EFCC ne suka gurfanar da ’yan Yahoo din a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume masu alaka da zamba cikin aminci, yaudara da kuma damfara.
- Ana Matsa Mana Mu Yi Magudin Zabe —CDS
- An zabi ’yar Najeriya cikin ’yan jaridar duniya da za su samu horo na musamman
Bayan gurfanar da su gaban kotu, wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu.
Sai dai lauyan masu shigar da kara, K.U. Udus da I.K. Agwa ya roki kotu da ta yanke musu hukuncin da ya dace.
Mai shari’a Ikponmwonba ta yanke wa uku daga cikinsu hukuncin daurin shekara uku a gidan yari tare da zabin biyan tarar Naira 200,000.
Na hudu kuma aka yi masa daurin shekara biyu a gidan yari ko kuma ya biya tarar Naira 200,000.
Kotun ta dage sauraren karar har zuwa ranar 10 ga watan Janairun 2023.