✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Kotu ta aike da Sheikh Abduljabbar gidan yari

An tuhumi malamin da furta kalaman batanci ga Annabi da sahabbansa

Wata Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a birnin Kano ta aike da malamin nan,  Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara gidan yari.

Hukuncin dai ya biyo bayan gurfanar da shi da gwamnatin Jihar ta yi tana tuhumar sa da aikata sabo.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Malam Muhammadu Garba, ya ce tuhume-tuhumen da aka gurfanar da malamin, wanda ake zargi da furta kalaman batanci a kan sahabbai da Manzon Allah (SAW), kansu sun hada da  ta da zaune-tsaye.

“Wannan ya biyo bayan samun rahoton binciken farko daga ’yan sanda ne da Ofishin Antoni-Janar, kuma Kwamishinan Shari’a, ya yi”, inji Malam Muhammad Garba.

“Daga bisani an gurfanar da shi ranar Juma’a, 16 ga watan Yuli a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Kano, karkashin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, inda aka karanta masa laifuffukan da ake zargin sa da su.”

Sanarwar ta kara da cewa bayan zaman kotun, alkali ya ba da umarnin ci gaba da tsare shi a hannun ’yan sanda har zuwa ranar Litinin mai zuwa inda za a aike da shi gidan yari.

Hakan dai na nufin malamin zai ci gaba da zama a kulle har zuwa ranar 28 ga watan Agusta da za a dawo domin ci gaba da shari’ar.

A makon da ya gabata ne dai Sheikh Abduljabbara ya yi mukabaka da Malaman Kano – sai dai an tashi taron ba tare da an cimma matsaya ba.

Daga bisani kuma Sheikh Abduljabbar ya nemi gafara kan kalaman da suka jawo shirya mukabalar tun da farko, inda ya ce ba a fahimce shi ba ne kuma ya janye su, ko da yake Gwamnatin Kano ta ce neman gafarar tasa bai cika ka’ida ba.

A watan Fabrairun daya gabata, gwamnatin ta sanar da rufe masallacinsa tare da haramta masa yin wa’azi har sai abin da hali ya yi.