✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta aike da matasan da suka kone ofishin INEC kurkuku

Ana zargin matasan da kone ofishin INEC a lokacin zaben shugaban kasa a Karamar Hukumar Takai

Kotun Majistare da ke zamanta a Gyadi-gyadi a Jihar Kano ta tisa keyar matasan da ake zargi da kona ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Karamar Hukumar Takai, a lokacin zaben shugaban kasa zuwa gidan yari.

Mai gabatar da kara, lauyar gwamnati, Barista Hajara Ado Sale ta shaida wa kotu cewa a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023 matasan suka kone ofishin INEC da ke garin Takai, lamarin da ya janyo asarar dukiya.

A cewar Barista Hajara, laifukan da ake zargin matasan da aikatawa na hadin baki da lalata dukiya sun saba da sashe na 97 da 121 na Kundin Dokar Hukumar INEC ta shekarar 2022.

Sai dai dukkaninsu sun musanta aikata laifin da ake zargin su da shi, inda mai gabatar da kara ta roki kotun da ta tsare su har zuwa lokacin da za su sami shawarwarin gwamnati a kan lamarin.

Alkalin kotun, Mai shari’a Mustapha Sa;ad Datti, ya ba da umarnin a tsare wadanda ake zargin a gidan gyaran hali sannan ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Maris, 2023.