Wata kotu a kasar Peru ta aike da kanwar matar Shugaban Kasar, Pedro Castillo, gidan kurkuku na wata 30 saboda zarginta da wata badakalar kwangiloli.
Kotun dai a ranar Lahadi ta aike da matar mai suna Yenifer Paredes, wacce shi da matarsa suka raina tun tana yarinya a gidansu.
- HOTUNA: Yadda Rarara ya raba motoci da wayoyi a gasar wakar Tinubu
- ASUU ta sake tsawaita yajin aikinta
Masu shigar da kara dai Yenifer na daya daga cikin wadanda suke da hannu a badakalar kwangiloli a yankinsu na Cajamarca da ke kasar.
An dai zarge ta ne da aikata badakalar kuma za ta kasance a gidan kurkukun har zuwa lokacin da za a kammala binciken.
Shugaba Pedro dai wanda ya shafe wata 13 a karagar mulki ya sha fama da zarge-zargen rashawa, kuma ya tsallake yunkurin tsige shi har sau biyu.
Sai dai ya musanta hannu a zarge-zargen wadanda ya bayyana a matsayin wata hanya da ’yan adawa ke kokarin yin amfani da ita wajen tsige shi.
Masu shigar da karar sun kuma bukaci a a hana matar Shugaba Pedron, Lilia Paredes, kowacce irin tafiya a wajen kasar na tsawon shekara uku masu zuwa.
Kodayake masu shigar da kara sun dada matsa kaimi wajen tsitsiye iyalan Shugaban, amma ba za su iya tsare shi ko gurfanar da shi ba matukar yana kan kujerar.