Kotu ta yanke wa wani matashi mai shekara 24 hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Mai Shari’a Oluwatoyin Abodunde, ta yanke masa hukuncin ne a ranar Talata bayan kama shi da laifin aikata fashi da kuma fyade da ake tuhumar sa da aikatawa.
- Kifi ya hadiye dan ninkaya ya amayar da shi da rai
- Za a rataye ’yan bindiga da masu satar mutane a Neja
Kotun da ke zamanta a garin Ado Ekiti, hedikwatar Jihar Ekiti, ta ce laifuka uku da ake tuhumar sa da aikawata sun tabbata, “An kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya; Allah Ya jikan sa.”
Laifukan da kotun ta kama shi da aikatawa na da alaka da fashi da makami da kuma fyade a ranar 30 ga watan Oktoba 2015, a layin Oda Ponna, da ke unguwar Omuo Ekiti.
Baya ga ayyukan fashi, matsalar fyade ta kazanta a sassan Najeriya, wanda ya kai ga kira-kirayen yanke hukunci mai tsauri ga masu aikatawa domin zama izina ga masu mummunar dabi’ar.
A kan haka ne wasu jihohi suka kafa dokar yanke hukuncin kisa ko daurin rai-da-rai ko dandaka ga masu aikata fyade.