✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu na neman matar shugaban kasar Zimbabwe

Har yanzu Uwargidan shugaban kasar Zimbabwe Grace Mugabe ta ki bayyana gaban wata kotun Afirka ta Kudu bisa tuhumar far wa wata matashiya da ta…

Har yanzu Uwargidan shugaban kasar Zimbabwe Grace Mugabe ta ki bayyana gaban wata kotun Afirka ta Kudu bisa tuhumar far wa wata matashiya da ta yi duk da yake jami’ai sun ce za ta je.

‘BBC ta ruwaito cewa ‘yan sandan kasar da yammacin ranar Talata sun ce ba su san inda matar shugaban kasar Misis Mugaben take ba.

Wata matashiya ‘yar shekara 20 ce a Afirka ta Kudu ta zargi uwargidan shugaban Zimbabwe da shauda mata wayar lantarki a ka yayin wata tashin-tashina a wani otel.

Ta kuma sanya wani hoton rauni a fuska a shafin sada zumunta. Zargin da har yanzu uwargidan Mugaben ta ki cewa uffan ba.

Gabriella Engels ta zargi Grace Mugabe, mai shekara 52, da zabga mata waya a fuska bayan ta same ta da wasu ‘ya’yanta guda biyu a wani dakin otel da ke Sandton.

Al’amarin ya faru ne da maraicen ranar Lahadi. 

Tun da farko, ministan ‘yan sandan Afirka ta Kudu ya ce uwargidan shugaban kasar Zimbabwe, Grace Mugabe, za ta gurfana a gaban kotun game da rahotanni kan zargin cin zarafi.

Fikile Mbalula ya ce: “Ba a kama Misis Grace ba saboda ta ba da hadin kai kuma ta mika kanta ga ‘yan sanda.”

‘Yan sandan Afirka Ta Kudu sun tabbatar cewa matashiyar ta kai rahoton far mata da nufin cutarwa.