Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta ce korar ma’aikatan Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) kan shigarsu yajin aiki harantacce ne.
ASUU reshen Jami’ar KASU ta bayyana hakan ne bayan Gwamnatin Jihar Kaduna ta kori ma’aikatan Jami’ar 18 kan shigarsu yajin aikin da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta gudanar a jihar.
- Hanyoyin da za a bi don magance matsalar tsaro — Janar Kukasheka
- Zan kawo karshen rikicin Fulani da Makiyaya a Najeriya — Yariman Bakura
“Korar ma’aikata 18 saba yarjejeniyar da aka kulla ne tsakanin NLC da Gwamnatin Kaduna a ranar 20 ga Mayu 2021, wadda ta bayyana karara cewa babu ma’aikacin da za a yi wa zagon kasa saboda ya shiga yajin aikin da kungiyar ta kira,” inji kungiyar.
Shugaban Jami’ar ne ya sanar da korar ma’aikatar bisa umarnin Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ta hannun Kwamishinan Ilimi.
NLC ta gudanar da yajin aiki da zanga-zangar lumana ne domin neman gwamnatin jihar ta janye sallamar da ta yi wa ma’aikata 4,000, bisa hujjar cewa kudaden da take kashewa wurin biyan albashi sun wuce misali.
Shugaban ASUU, reshen Jami’ar, Kwamared Peter Adamu da Sakataren Kungiyar Silas Akos, sun ce sabanin ikirarin da hukumar gudanarwar jami’ar ke yi, babu wata takardar neman bahasi da aka aike wa ma’aikatan da ita balantana su fuskanci wani kwamitin ladabtarwa.
Kungiyar ta kuma zargi Gwamnatin Jihar da umartar a dakatar da bayar da kudaden kungiyoyin kwadago da ake cira da albashin ma’aikata.
Matakin, a cewar kungiyar ya saba wa Dokar Kwadago ta 2005 wadda ta bayyana tare da halastawa karara cewa a ciri kudaden daga albashin ma’aikata a kuma bayar da su ga kungiyoyin kwadago.
Ta ce dokar ta tanadi cirar kudaden kai tsaye daga albashin duk mambobin kunyoyin kwadago a mika su ga kungiyoyin, ba sai da amincewar wanda suke yi wa aiki ba.