Daruruwan masu zanga-zanga sun fito kan tinutuna bayan wasu ‘yan gwagwarmaya sun kona Alkur’ani a birnin Malmo na kasar Sweden.
Zanga-zangar ta barke ne bayan kona Alkur’anin a ranar Juma’a, lamarin da ya sa daruuwan mutane kona tayoyi da sauran abubuwa domin nuna bacin rai a titunan yankin Rosengard da ke Kudancin kasar.
An yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da ‘yan sandan kwantar da tarzomar da dare, inda suka yi ta yi wa ‘yan sandan ruwan duwatsu har suka raunta wasu daga cikin jami’an ‘yan sanda.
Kamfanin dillanci labaru na AP ya ce an ‘yan sanda na tsare da akalla mutum 15 daga cikin masu zanga-zangar.