✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Matasa ta Ƙasa ta goyi bayan taron Kur’ani

Malaman da ba sa goyon bayan wannan taro su sani cewa, “wannan ba taron siyasa ba ne.”

Ƙungiyoyin alarammomi da matasa daga jihohin Arewa sun nuna goyon bayansu a kan taron karatun Kur’ani na ƙasa da ake shirya gudanarwa a Abuja a ranar 22 ga watan Fabrairu.

Shugaban ƙungiyoyin, Kwamred Murtala Mohammed Garba, wanda aka fi sani da Gamji, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya bayyana cewa, suna yaba wa shugabannin Musulunci da suka shirya wannan taro kamar su Sarkin Musulmi, Imam Dahiru Usman Bauchi da Sheik Karibullah, da kuma Sheik Bala Lau.

Ya ce, irin wannan taro na masu kishin Kur’ani, wanda ba a taɓa yin irinsa ba a Nijeriya, inda alarammomi dubu talatin da suka haddace Kur’ani, zai haɗa kan al’umma ya kuma karfafa alaƙa da zaman lafiya da zamantakewa a tsakanin al’ummar Musulmi baki daya.

Kwamred Gamji ya kuma yi kira ga malaman da ba sa goyon bayan wannan taro da cewa, “wannan ba taron siyasa ba ne.

“Saboda haka su ajiye kishi da bambance-bambance a gefe guda don ci gaban Musulunci.”

Hakazalika, ƙungiyoyin sun kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan goyon bayan da ya bayar ga wannan taro da kuma kafa Hukumar Kula da Almajirai a Nijeriya.

Ya ci gaba da cewa, Kur’ani na kowa ne, saboda haka Musulmi su haɗa kai baki ɗaya saboda ci gaba taron zai kawo.