Almajirai 1,500 sun samu kyautar sabbin rigunan sanyi da sauran kayan sanyi, a wani kokari na kare kananan yara daga illar sanyin damuna a Jihar Yobe.
Da take rabon kayan sanyin ga makarantun tsangaya 271 da suka amfana da tallafin, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) ta ce gwamnatin jihar ta sha alwashin rungumar makarantun tsangaya da nufin zamanantar da tsarin karatunsu da kuma ba su kulawar da ta dace.
A ranar biyu a watan Agusta, 2021 ne gwamnan jihar, Mai Mala Buni ya umarci Hukumar ta samar da sabbin kayan sanyi ga almajirai 1,500 a makarantun tsangaya 271 da ke wasu kananan hukumomi bakwai na jihar.
Makarantu allon na Kananan Hukumomin Gujba da Fune da Pataskum, Damaturu, Nguru, Gashua da kuma Geidam.
Babban Sakataren Hukumar, Dokta Muhammad Goje, ya ce gwamnatin za ta ci gaba da tallafa wa almajirai domin kare su daga sanyi da kuma shigar da su cikin tsarin karatu da ya dace da zamani.
A cewarsa, an yi rabon tallafin ne don malaman tsangayar su gamsu cewa tsarin zamanin da ake so a shigo da shi cikin harkar makarantun allo mai amfani ne.
Hakan, a cewarsa, zai ba wa masu ruwa da tsaki damar shigo su ba da tasu gudunmawar don samun nasarar kudurin na gwamna Mai Mala Buni.
A jawabansu, malaman makarnatun tsangayar da suka samu kyautar kayan sanyin sun yaba da kokarin gwamnatin jihar kan yadda take tallafa wa almajirai a findin jihar.
A cewarsu, da farko, suna dar-dari, amma tun a lokacin sallah da aka zo musu da kayan sallah da abincin almajiran suka saki jiki suka yarda cewa da gaske gwmnatin take.
Daya daga cikin alarammomin, Malam Goni Umar, ya ce sun ji dadi matuka da yadda Gwamna Buni ya cika alkawarin da ya yi musu na cewa zai taimake su kuma yanzu suna gani a zahiri.