✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin kalubale na Ingila: Gobe Man United da Tottenham, jibi kuma Chelsea da Southampton

A ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin kalubale na Ingila (FA) a gobe Asabar kulob din Manchester United zai kece raini da na…

A ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin kalubale na Ingila (FA) a gobe Asabar kulob din Manchester United zai kece raini da na Tottenham a wasan kusa da na karshe (Semi-Fainal).  Wasan zai gudana ne da misalin karfe 5 da kwata na yamma agogon Najeriya. Sannan a jibi Lahadi ne za a yi wasa a tsakanin kulob din Chelsea da na Southampton a daya wasan na semi-fainal kuma wasan zai gudana ne da misalin karfe 3 na rana agogon Najeriya.  kungiyoyi biyun da suka samu nasara a wasanni biyun ne za su hadu a wasan karshe a wata raan da Hukumar shirya kwallon kafa a Ingila (FA) za ta sanar nan gaba kadan.

Dukkan kungiyoyin hudu suna yunkurin lashe wannan kofi ne don gudun kada su tashi a tutar babu a kakar wasa ta bana ganin yadda tuni kulob din Manchester City ya lashe kofin firimiya da kuma na Carabao (Carling cup) sai dai an fitar da kulob din a gasar cin kofin kalubale na bana.