✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin Duniya na 2018: Za mu gayyato ’yan wasa 35 – Rohr

Manajan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Gernot Rohr ya ce zai yi amfani da ’yan wasa uku zuwa hudu a kowane mataki a…

Manajan kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles, Gernot Rohr ya ce zai yi amfani da ’yan wasa uku zuwa hudu a kowane mataki a shirye-shiryen da yake yi don halartar gasar cin Kofin Duniya da za a fafata a Rasha a bana.

Rohr wanda ya halarci gasar cin Kofin Afirka na ’yan wasan gida (CHAN) da aka kammala a Moroko a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce akwai dimbin aiki a gabansa kafin ya fitar da jerin ’yan wasa na karshe da za su halarci gasar ta duniya. Sai dai ya ce za a ba ’yan wasan gidan dama domin su nuna kwazonsu kamar yadda suka nuna a kasar ta CHAN.

 Jaridar wasanni ta Complete Sports ta ruwaito Rohr yana cewa,  “Dabarar ita ce a samu ’yan wasa uku a kowane matsayi a sansanin horo inda daga nan za a dauki bibbiyu da suka fi cancanta da kuma uku daga cikin masu tsaron gida don zuwa gasar cin kofin Duniya a Rasha. Kuma wadansu daga cikin ’yan wasan gidan da suka fafata a gasar CHAN a Moroko za su halarci sansanin saboda rawar da suka taka a gasar ta Afirka.”  

Rohr ya ce yana da burin ganin Najeriya ta tsallake zuwa wasan Kwata-Fainal na gasar ta duniya, don haka kwararrun ’yan wasa ne kawai za su wakilci kasar nan a gasar.

“Burinmu mu kai wasan Kwata-Fainal a gasar Kofin Duniya, saboda wannan dalili za mu dauki ’yan wasan da suka fi cancanta ne kawai, wadanda suke da kazar-kazar da iya taka leda. Muna da tsare-tsare masu kyau don zuwa Rasha wajen gudanar da wasannin sada zumunta daban-daban da za su yi mana tasiri a gasar ta duniya.

 Kocin ya nuna jin dadinsa kan rawar da masu tsaron gidan Najeriya a gasar ta CHAN, Ikechukwu Ezenwa da Dele Ajiboye.