✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin Afirka na mata: Najeriya za ta kece-raini da Afirka ta Kudu a wasan farko

Najeriya ta lashe gasar sau tara, inda ta fito gaba-gadi domin neman lashe gasar karo na 10.

A Litinin din nan ne tawagar Super Falcons ta Najeriya za ta fafata da tawagar Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu a wasan farko na Gasar Cin Kofin Afirka ta Mata ta bana.

Za a fafata wasan ne a Filin Wasa na Rabat, babban birnin kasar Moroco da misalin karfe shida na yamma.

Idan ba a manta ba, Najeriya ce ta doke Afirka ta Kudu a wasan karshe na gasar ta shekarar 2018 a bugun fanareti.

Sai dai kuma wata goma baya, tawagar Banyana Banyana ta zo har Najeriya, inda ta lashe Gasar Kofin Aisha Buhari, inda ta doke Najeriya da ci hudu da biyu a Filin Wasa na Mobolaji Johnson da ke Jihar Legas.

Najeriya ta lashe gasar sau tara, inda ta fito gaba-gadi domin neman lashe gasar karo na 10.

‘Yan wasan da za su fara wasan: