Tawagar kwallon kafar mata ta Najeriya ta Super Falcons ta Lallasa takwararta ta kasar Kamaru a ci gaba da gasar cin kofin mata ta nahiyar Afirka da ke gudana a kasar Maroko.
Hakan dai na nufin Najeriya ta cancanci buga gasar cin kofin duniya ta mata da za a yi a shekarar 2023.
- Mun lalata gonakin Tabar Wiwi masu fadin hekta 2 a Imo – NDLEA
- LABARAN AMINIYA: Fulani Da Irigwe Sun Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya
uper Falcons of Nigeria have beaten the Lionesses of Cameroon 1-0 to qualify for the semi-final of the ongoing Africa Women’s Cup of Nations in Morocco.
Najeriya dai ta lallasa Kamarun ne da ci daya mai ban haushi, bayan ’yar wasanta, Rasheedat Ajibade ta jefa mata kwallo bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Dukkan kasashe hudun da suka je matakin kusa da na karshe a gasar dai sun cancanci buga gasar cin kofin duniya da kasashen Austalia da New Zealand za su dauki bakincinta a 2023.