Tawagar Banyana Banyana ta kasar Afirka ta Kudu ta doke takwararta ta Super Falcons ta Najeriya da ci biyu da daya.
A wasan wanda shi ne na farko a Gasar Cin Kofin ta Mata wato WAFCON, Afirka ta Kudun ta fanshe doke ta da Najeriya ta yi a wasan karshe na gasar ta karshe da aka buga a shekarar 2018.
- Jerin tafiye-tafiyen da Buhari ya yi zuwa ketare a bana
- Miji ya kona matarsa har lahira saboda kin komawa gidansa
Bayan zuwa hutun rabin lokaci babu ci, tawagar Banyana Banyana ta mamayi Super Falcons, inda ta zura mata kwallo biyu a jere a raga.
Jermaine Seoposenwe ce ta fara jefa kwallo a ragar Najeriya a minti 61 da fara wasa, sai minti 68 da fara wasa Hildah Tholakele Magaia ta kara kwallo na biyu.
Sai daga bisani ’yar wasan Najeriya da ke taka leda a kungiyar Atletico Madrid ta Spain, Rasheedat Ajibade ta farke kwallo daya a minti 91 da fara wasa.
Da wannan sakamakon, Najeriya za a iya cewa ta fara kafar hagu a shirinta na kare kambunta na gasar, da kuma kokarinta na lashe gasar karon na goma.
An buga wasan ne a Filin Wasa na Rabat, Babban Birnin Kasar Morocco.