Saboda da nasarar da kulob din Leicester City na Ingila ya samu na lashe gasar rukunin firimiyar Ingila, kocinsu Claudio Raneri ya samu kyautar Fam miliyan 5 kwatankwacin Naira biliyan 2 da miliyan 345.
A kwantaragin da kocin ya sanya wa hannu a watan Yunin 2015 na tsawon shekaru uku, an nuna kocin zai samu wannan kyauta ce idan ya samu nasarar lashe kofin firimiya don haka yanzu da abin ya tabbata ne ake sa ran kocin zai karbi wannan kudi a matsayin kyauta (bonus). Sannan kulob din ya fara yunkurin sabunta kwantaragin kocin da zarar an kammala kakar wasa ta bana don ganin ya cigaba da horar da kulob din.
Rahotanni sun nuna kasar Italiya ta fara zawarcin Claudio Raneri don ya zama kocinta baya ga wadansu kungiyoyin kwallon kafa daban-daban da suke zawarcinsa.
Sai dai sauran ’yan kwallon kulob din ba za su samu irin wannan kyauta ba saboda babu inda aka yi musu tanadin haka a kwantaragin da suka sanya wa hannu.
Leicester City dai ta kafa sabon tarihi bayan ta lashe kofin firimiya a karon farko a tarihin kulob din a tsawon shekara 132 da kafa shi.
…Kocin Leicester City ya samu kyautar Naira biliyan biyu
Saboda da nasarar da kulob din Leicester City na Ingila ya samu na lashe gasar rukunin firimiyar Ingila, kocinsu Claudio Raneri ya samu kyautar Fam…