Kocin Ingila, Gareth Southgate, ya caccaki tsarin amfani da na’urar taimaka wa alkalin wasa na bidiyo (VAR) saboda mummunan tasirin da take yi ga magoya bayan wasan.
A bayan nan dai masu lura da na’urar VAR sun kasa sauya hukunci lokacin da aka yi kuskuren soke wata kwallo a wasan da Tottenham ta yi nasara a kan Liverpool a ranar Asabar ɗin da ta gabata.
- FIFA ta bayyana kasashen da za su shirya gasar cin kofin duniya ta 2030
- Mai tabin hankali ya kashe mutum 8 a Adamawa
Southgate ya bayyana dalilin da ya sa ba ya son VAR a ranar da ya bayyana tawagarsa ta Ingila a wasannin da za ta yi da Australia da Italiya.
Duk da haka ya yarda da cewa kwallon kafa ba za ta koma zamanin da ba a amfani da fasaha wurin yanke hukunci ba.
Da yake karin haske game da yadda yake ji game da VAR, Southgate ya kara da cewa, “Abin da zan ce shi ne a wancan lokacin kowa ya kan je mashaya ya yi korafi game da alkalin wasa kuma har yanzu suna zuwa mashaya suna korafi kan alkalin wasa, har yanzu babu abin da ya canza.”
A sake wasanmu da Tottenham — Klopp
Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp na son a sake wasan Firimiyar da ya gudana ranar Asabar tsakanin ƙungiyarsa ta Liverpool da Tottenham.
Tottenham ce ta yi nasarar cin 2-1 a karawar ta mako na bakwai da Liverpool ta kammala fafatawar da ’yan kwallo tara a cikin fili.
Klopp ya bukaci a sake wasan ne bayan da alkalan da suka kula da na’urar VAR suka yi kuskuren soke kwallon da Luis Diaz ya ci, kan cewar an yi satar gida.
Darren England da Dan Cook ne suka kula da na’urar VAR a karawar da kungiyar Anfield ta ci gida daf da za a tashi ta hannun Joel Matip.
“Wani abu makamancin haka bai kamata ya faru ba a gasar Firimiya, saboda haka nake tunanin ya dace a sake wasan,” in ji Klopp.
To sai dai masu ruwa da tsaki sun fahimci cewar hukumar da ke kula da gasar ta Firimiya ba ta da wata madogarar da za ta amince a sake wasan, sannan babu tabbas ko Liverpool ta rubuta bukatar hakan a rubuce.
Wadanda suka tafka kuskuren a wasan na Tottenham da Liverpool ba sa cikin alkalan wasan da za su yi alƙalanci a wasannin gasar Firimiya da za a buga a karshen makon nan.
Lamarin na zuwa ne bayan an bukaci England da Cook da su hutu, sakamakon kuskuren da suka tafka a karawar ta hamayya.
Wadanda suka hura wasan na Tottenham da Liverpool, Simon Hooper shi ne zai kula da VAR a fafatawar Bournmouth da za ta je gidan Everton ranar Asabar.
Shi kuwa Michael Oliver, wanda shi ne ya yi jiran ko-ta-kwana zai ja ragamar karawa biyu a karshen makon.