✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kocin Eagles zai yi murabus

Rahotanni da ke fitowa sun nuna kocin Super Eagles Gernot Rohr ya fara tunanin ajiye aiki saboda kallon hadarin kajin da Hukumar NFF take yi…

Rahotanni da ke fitowa sun nuna kocin Super Eagles Gernot Rohr ya fara tunanin ajiye aiki saboda kallon hadarin kajin da Hukumar NFF take yi masa tun bayan da Afirka ta Kudu ta lallasa Najeriya da ci 2-0 a gasar neman hayewa gasar cin kofin Afirka da aka yi a garin Uyo na Jihar Akwa Ibom a watan jiya.

Rahoton ya ce jim kadan bayan an kammala wasan ne sai kwamitin zabo ’yan kwallo na Super Eagles ya nemi tattaunawa da kocin inda nan take ya gindaya wa kocin wadansu ka’idojin da ba su yi wa kocin dadi ba.  Daga cikin ka’idojin akwai sai kwamitin ya rika amincewa da kuma tantance duk sunayen da kocin ya zabo kafin su yi wa Eagles kwallo.

Haka kuma kwamitin ya nemi ya yi wa kocin wadansu gyare-gayare a game da yadda yake tafiyar da harkar kungiyar, al’amarin da wadannan matakai da kwamitin ya dauka suka bakanta wa kocin rai.

Rahoton ya nuna wani na hannun daman kocin ne ya kyankyasa wa kafar watsa labarai ta Naij.com cewa kocin ya fara tunanin yin murabus ganin an fara yi masa katsalandan a harkar tafiyar da kungiyar Super Eagles.

Rahoton ya kara da cewa tuni Kocin ya yanke shawarar zama da kwamitin nan da ’yan kwanaki don tattaunawa, idan ba a samu maslaha ba, ko shakka babu zai ajiye mukaminsa horar da kungiyar.

Gernot Rohr dai ya fara shan suka ne tun bayan da Afirka ta Kudu ta lallasa Super Eagles a garin Uyo a watan jiya.