Mai magana da yawun tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya ce sam maigidan nasa bai yi wani abu don yi wa yunƙurin Bola Tinubu na zama Shugaban Najeriya a 2023 zagon ƙasa ba.
Ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata yayin wani taron manema labarai gabanin kaddamar da sabon littafin da ya rubuta a kan zamansa mai magana da yawun Buhari, wanda za a kaddamar ranar tara ga watan Yuli.
- ’Yan sanda sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Jigawa
- DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa
An dai yi zargin cewa da gangan Buhari ya jinkirta cire tallafin man fetur har zuwa karshen mulkinsa a 2023 domin ya hada ’yan Najeriya fada da Tinubu.
Kazalika, ’yan Najeriya sun rika sukar lamirin gwamnatin Tinubu kan kawo wahalhalu da yunwa tun bayan sanar da cire tallafin man da shugaban ya yi ranar da aka rantsar da shi.
To sai dai Garba Shehu ya karyata batun cewa an shirya cire tallafin ne saboda a yi wa Tinubu zagon kasa.
Kakakin ya ce ya cika da mamakin labarin, yana mai cewa ba yadda za a yi Buhari ya yi hakan ga dan jam’iyyarsa, tamkar daga wata jam’iyyar zai karbi mulkin daga hannunsa.
Ya ce, “Da Buhari da Tinubu duk ’yan APC ne, saboda haka ban ga ta yadda za mu shirya abin da zai yi wa gwamnatinmu zagon kasa ba.
“Buhari mutum ne da ya tsani harkar rashawa, ya shigo gwamnati da gaskiyar shi, kuma har ya gama a haka yake. Ya yi iya bakin kokarinsa ga ’yan Najeriya kuma tarihi ba zai manta da shi ba. shi ba mutum ba ne mai kwarmato, aiki kawai ya yi,” in ji Garba Shehu.
Ya kuma ce shi a karan kansa bai yi laifi ba saboda ya kyale tsohon maigidansa kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi aiki a gwamnatin Buhari.