✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ’yan majalisa ne matsalar kasa? (II)

Da  fari  an yi kitso da mugun zare, saboda haka ba za a shuka dusa ba, amma a sa ran za ta fitar da tsiro…

Da  fari  an yi kitso da mugun zare, saboda haka ba za a shuka dusa ba, amma a sa ran za ta fitar da tsiro ba. Wannan ne ya sa talakawa korafe-korafe da tsinuwa ga ‘yan majalisar a sakamakon rashin ganin wani amfani da ‘yan majalisun suke da shi gare su. Kuma shekara daya da ta wuce sai wadannan ‘yan majalisa suka kara dawo da wani yunkuri na samar da doka da za ta ba su rigar kariya daga gurfana a gaban shari’a kamar yadda gwamna da mataimakinsa da kuma shugaban kasa da mataimakinsa suke da ita. Sun yi makamancin wannan yunkurin a can baya, amma bai kai labari ba. Abin da ya sa suka kara dawo da yunkurin nasu yanzu, shi ne, gurfanar da Shugaban Majalisar Dattijai  Bukola Saraki da Gwamnatin Tarayya ta yi a kan zargjn ba da bayanai na karya da ya yi yayin bayyana kadarorinsa kafin fara aikinsa a matsayin sanata.

Ita kanta fa rigar kariya ta shugaban kasa da ta gwamnonin kasar, wacce ‘yan majalisun suke son kwaikwaya dauke take da tufka-da-warwara. Ma’ana, wani karamin sashe ya ba da rigar kariyar ga shugaban kasa da gwamnoni, wani babban sashe, wanda yake sawun giwa ne mai take duk wata doka a fadin Najeriya da ba  ta yi daidai da shi ba, ko da kuwa daga cikinsa ta fito, shi kuma ya take ko kuma ma in ce ya fizge rigar kariyar.

Sashe na 308 na tsarin mulkin 1999 ya ba da kariya ga gwamnoni da shugaban kasa da mataimakansu, amma shi kuma sashe na 1 shi dai wannan tsarin a karkashin babi na 1,  mai dauke da buwaya ga tsarin mulkin ya bayyana karara cewa dukkan ‘yan kasa daya suke a gaban doka ba wanda ya fi wani komai mukaminsa. Ka ga ke nan sashe na 308 ma haramtacce ne!

Ciki da gaskiya wuka ba  ta huda shi. Ma’ana idan ‘yan majalisa in suna da gaskiya ba za su ji tsoron gurfana a gaban shari’a a kan kowace tuhuma ba. Tun bayan tauna tsakuwa da gwamnatin tarayya ta yi, ta hanyar gurfanar da Shugaban Majalisar Dattijai Saraki da ta yi a kotun da’ar ma’aikata hankalin ‘yan majalisu ya tashi, domin ‘yar manuniya ce da ke nuna musu cewa gwamnatin tarayya fa ta bude wa ‘yan Najeriya kofar kai su kara a gaban kotu. Domin dakile hakan sai suka fara yunkuri fiye da shekara daya da suka wuce domin rufe kofar, ta hanyar yin doka da za ta hana gurfanar su a gaban alkali. 

A ganina, ai daman tuntuni ‘yan majalisa suna da kariya a tare da su. Misali, ana zabar mutum, ko kuma yana yin magudin zabe zuwa majalisa yake guduwa zuwa Abuja ya labe a can. Ba a kara ganin yawancinsu sai an kada gangar siyasa, za ka ga ba kunya babu tsoron Allah sun dawo da tarin jami’an tsaro kamar sun fito yaki, suna kwantar da kai suna bin masu rawani da malamai da sauran fitattun unguwanni suna ba da cin hanci da kuma rokon a kara zabarsu. Kariya ta biyu da suke da ita, ita ce, ana sukarsu a kan abin da suka yi da talaka ba ya amfana da shi, ko kuma shi talakan ba shi ya fi bukata ba, sai ka ga sojojin bakan su sun yi sauri suna kare su a kafafen yada labarai, domin ta hakan ne su kuma sojojin suke samun na sakawa a bakin salati. Wasu lokuta kuma sai su tura a je a yi ta yada farfaganda da karairayi domin wai talaka ya so su. Kariya ta uku ita ce, suna biyan makudan kudi ga lauyoyi da sukan ba su shawarwari domin kauce wa fuskantar shari’a a kotu. In kuma ma an kai kararsu to sai lauyoyinsu su yi sauri su je kare su. A wasu lokutan ma sukan saye alkalan domin samun nasara a shari’ar.

Yawancin ‘yan majalisa musamman na dattijai, tsofaffin gwamnoni wadanda suka amfana da rigar kariya lokacin da suke rike da mukamin gwamnoni ne, saboda haka yanzu idan aka bai wa ‘yan majalisa kariya, zai kasance bayan gwamna ya yi shekaru tawas a matsayin gwamna yana satar kudin talakawa, sai kuma ya tafi majalisa, inda ma a can zai more rigar kariya, har kusan ya bar duniya zai yi ta cin karensa babu babbaka, ba tare da an kalubalance shi a kotu ba. Yin hakan zai samar da tawaya ne ga jaririyar dimokaradiyyar Najeriya, domin ai kalubalantar ‘yan majalisa, kalubale mai ma’ana yana daga cikin turakan dimokuradiyya.

A madadin yin doka da ‘yan majalisa suke son yi domin samar wa kansu kariya, me zai hana su maida hankali wajen yin dokoki da za mu inganta rayuwar ‘yan gudun hijirar rikicin Boko Haram da kuma samar da wadatattun kayan aiki da walwala ga sojoji da ‘yan sanda da ke aikin samar da zaman lafiya a Maiduguri, da ma wadanda ke aiki a sauran jihohi? Me zai hana su yi doka da za ta rage tsadar kayan abinci? Me zai hana su yi doka da za ta yi sanadiyyar yawaitar likitoci da ‘yan sanda a Najeriya, domin samun zaman lafiya da ingantacciyar  lafiya? Me zai hana su yi doka da za ta kara mafi karancin albashin ma’aikata? Me zai hana su yi dokar da za ta mayar da karatun yara mata a kasar nan, dole kuma kyauta, daga firamare har zuwa jami’a? Me zai hana su karfafa dokokin hana bautar da yara? Me zai hana su yi dokar da za ta rage kashe kudin da ake a lokacin yakin neman zabe saboda haka talaka ma zai iya yin takara a zabe shi.

Mafita ita ce, talaka ya daina tsine wa ‘yan majalisa domin tsinuwar za ta kara bata ‘yan majalisun, kuma daga karshe a kan mai tsinuwar komai zai kare. Addu’ar shiriya ya kamata a rika yi musu. Sannan talaka ya farka daga bacci mai nauyi da, domin zabar  ‘yan majalisu gogaggun ‘yan book, wadanda suka iya yin magana da Turanci a gaban mutane ko da kuwa Turawa ne, kuma masu halayya tagari. Kuma talaka ya yi kokarin daina sayar da ‘yancinsa a lokacin zabe ya tuna cewa babu yawan kudin da dan siyasa zai iya ba shi ya sayi kuri’arsa, domin ita ce makamin kwatar kai a dimokuradiyance. Ya kamata talaka ya yi zabe ya tsaya, kuma ya raka kuri’arsa, kamar yadda ya yi a zaben Buhari na karshe kuma ya ga amfanin hakan. Ya kamata a samu yawaitar kungiyoyi masu zaman kansu kamar su CISLAC, domin bibbiyar ‘yan majalisa don tabbatar da cewa talakawa ne a gabansu ba son ran su ba. A soke majalisar wakilai, amma a bar majalisar dattawa, domin mu koma yin amfani da Majalisar Tarayya mai falle daya (unicameralism), kamar yadda manya-manyan kasashen duniya da tun tuni suka ci gaba kamar su China da Norway da New Zealand da Turkiya da sauran su suke yi. Yin hakan zai rage barnatar da kudin kasa ba tare da hujja ba. Talakawa su rika tara kudi suna daukar nauyin talaka dan uwansu da ya cancanta ya zama dan majalisa,  kuma su zabe shi, ba wai jira za su yi ba sai wani wanda bai san matsalolin su ba ya ciko jakar sa da kudi sannan ya zo ya ce su zabe shi. 

A karshe ya kamata su ma rassan mulki na Shari’a da na Zartarwa su rika daidaita sahun ‘yan majalisar yayin da suka kauce hanya, kamar yadda sassa na 5 da 6 na tsarin mulkin 1999 suka ba su dama. Ya kamata talakawa su rika yi wa ‘yan majalisu da ba sa yi musu wakilci mai kyau kiranye, domin sashe na 69 na dokar kasa na 1999 ta basu damar yin haka!

Bello Sagir marubuci ne daga Kano 08132518714