✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya dace Majalisun Tarayya su amince da neman karin kudin da Jonathan yake nema?3

A ’yan kwanakin nan, ana ta kai ruwa rana tsakanin Majalisun Tarayya da kuma Fadar Shugaban kasa Goodluck Jonathan game da kasafin kudin bana, wanda…

A ’yan kwanakin nan, ana ta kai ruwa rana tsakanin Majalisun Tarayya da kuma Fadar Shugaban kasa Goodluck Jonathan game da kasafin kudin bana, wanda ya yi wa kwaskwarima ya aika musu domin a kara masa kudi akan kasafin kudin bana. Majalisun sun cije cewa ba za su sanya masa hannu ba, shi kuma ya nuna bukatar su yi haka. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace majalisun su sanya masa hannu? Ga ra’ayoyin ’yan Najeriya:

Bai dace a sanya masa hannu ba – Buhari Kumurya
Malam Buhari Yunusa Kumurya: “A nawa ra’ayin, bai dace ’yan majalisar dokokin su sa hannu a kasafin kudin ba. Saboda kamar yadda ka sani, wadannan ’yan majalisa mutane ne da suke wakiltal jama’a daban daban a kasar nan. Watakilla akwai wani abu da suka hango a cikin wannan kasafin kudi da shugaban ya gabatar musu da suke ganin sa hannu ciki ka iya shafar al’ummar kasa baki daya ta hanyar da ba ta dace ba. Saboda haka ya kamata su bangaren zartarwar su tabbatar sun magance matsalolin kafin ’yan majalisar su sa hannu.”