✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko wane darasi ’yan Arewacin Najeriya za su dauka daga Sudan Ta Kudu?

wannan makon, mun samu tsokaci mai take na sama daga kwararren mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Yasir Ramadan Gwale, mai adireshin I-mel:…

Kungiyar Matasan Gizago na Jihar Bauchi ne nan, a Lahadin da ta gabata, a lokacin da suke shirin buga kwallon sada zumunta da Kungiyar Zantukan Soyayya ta Bauchi. An tashi Gizago na da ci uku da nema.wannan makon, mun samu tsokaci mai take na sama daga kwararren mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Yasir Ramadan Gwale, mai adireshin I-mel: [email protected] Ga abin da yake cewa game da al’amuran da suke faruwa a jaririyar kasar Sudan Ta Kudu:
Abin da ya faru a makon da ya wuce na barkewar rikici a tsakanin jaririyar kasar Sudan Ta Kudu ya zo wa da mutane da dama da bazata. Kamar yadda galibin al’ummar Kudancin Sudan suka dinga korafin cewar Larabawan da suke mulki a dunkulalliyar kasar Sudan sun ware su, kuma an hana musu dama ta yin rawar gaban hantsi, irin wannan zance da sauran zuga da dama ta sanya al’ummar da ke zaune a Sudan Ta Kudu suka jefa kuri’a da gagarumin rinjayen ballewa daga kasar Sudan, bayan da Shugaba Omar Hasan Albashir ya ba su damar kasancewa a dunkulalliyar Sudan ko kuma ballewa. Wannan ta sanya galibin kabilun wannan yanki suka zabi ballewa daga Sudan.
Wannan ballewar tasu ta zama tofin Allah-tsine ga tsohon jagoransu, John Garang, wanda ya tsaya kai da fata wajen ganin al’ummarsa ba su balle daga Sudan ba; duk kuwa da zuga da matsin lamba da yake sha daga kasashen waje a kan yin hakan.
Bayan mutuwar Garang a wani yanayi mai cike da ayar tambaya, wanda dan kabilar Dinka ne masu rinjaye, aka nada Silba Kiir a matsayin sabon magajinsa kuma shugaban al’ummar Kudancin Sudan a Gwamnatin Bashir da ke Khartoum. Kiir, shi ma dan kabilar Dinka ne, wannan kabila ita ce mafiya rinjaye a cikin dukkan kabilun da suke zaune a wannan yanki na Kudancin Sudan. Sun ninka kabilun Nuer da Meseriya da sauransu yawa nesa ba kusa ba.
kabilar Nuer su ne suke biye wa Dinka wajen yawan jama’a a Kudancin Sudan. Amma wani abin sha’awa shi ne, su kabilar Nuer duk da rashin rinjayen su a kasar amma su ne suke da rinjayen wadanda suka yi karatun boko. Wannan ta sanya suka fi dukkan kabilun yankin wayewa da saukin lamari.
Shi wannan Shugaba Silba Kiir, mutum ne da ya taso a gaba dayan rayuwarsa bai san komai ba sai yaki da zaman kadaici a cikin daji, irin na sojoji. Don haka ko makaranta bai yi ba da za ta ba shi damar gogewa da kuma gogayya. A saboda haka ne, a lokacin da suka samu ’yancinsu daga Sudan kuma ga arzikin man fetur Allah Ya huwace musu, aka yi ta fadi-tashin kafa gwamnatin hadin kan kasa, a Naibasha ta kasar Kenya. Suka cimma yarjejeniya da kabilar Nuer wajen tafiya tare, don gina sabuwar kasar tasu mai cike da kalubale.
Tun farkon kamun ludayin Gwamnatin Kiir, masu sharhi suka fahimci cewar lallai ba zai jima ba za a samu gagarumar baraka a cikin gwamnatinsa. Domin na farko, kamar yadda na fada, bai yi karatu ba kuma ba shi da wata wayewa ko gogewa da za ta bashi damar hada kan al’ummar kasar. Dan haka ne ba shi da wani aiki face daukar zuga ko abin da aka sanya shi yi daga kasashen da suke hankoron kwadayin man fetur din da kasar take da shi.
Yana daga cikin dalilin da ya sanya a karon farko ya samu sabani da ’yan kabilar Nuer din da ke cikin gwamnatinsa. Domin sun fahimci cewa babu inda shugaban ya sa gaba, face tara dukiyar haramun da kuma jiran umarni daga kasashen waje. Matsin lamba da caccakar da ’yan kabilar Nuer da ke cikin gwamnatinsa ta sanya rana a tsaka ya bayar da sanarwar korar jami’an gwamnatinsa gaba daya! Abin da ba a taba yi ba a duniya. Wannan al’amari ya harzuka ’yan kabilar Nuer bisa jagorancin mutumin da shi ne mataimakin shugaban kasa, Reak Machar. Shi Reak mutum ne dan book, wanda ya yi ilimin zamani mai zurfi kuma gogagge ta fuskar mu’amala.
***
Hidindimun Gizagawan zumunci:
A labarin farin ciki, a gobe ne za a daura auren Bagizage Mukhtar Jarmajao (08069634182), da misalin karfe 11:00 na safe, a Babban Masallacin Juma’ar Gombe.
Bagizage Malam Sulaiman Mai Bazazzagiya (08067917740), zai aurar da diyarsa, Malama Maryam Sulaiman, a gobe Asabar da misalin karfe 2:30 na rana, a Unguwar Maigwado, Sabon Gari, Zariya-Jihar Kaduna.
Muna rokon Allah Ya sa a yi cikin sa’a, Ya ba da zaman lafiya da zuri’a dayyiba. Gizagawan da ba su da aure, muna rokon Allah Ya ba su. – Gizago.
Shi kuwa daya daga cikin iyayen Gizagawan Jihar Nasarawa, Zanwan Lafiya, Alhaji Abdul’aziz Zakari (08096430960), ya samu karuwar haihuwar ’ya mace a makon jiya.
Muna rokon Allah Ya raya, Ya sa mai jinkan iyaye ce, amin. – Gizago.
A batun rijista kuwa, insha Allahu za mu ci gaba a makon gobe. Duk wanda ya aiko da bukatar neman rijista, sai ya kara hakuri. Mun gode. – Gizago.