Babbar Kotun Jihar Akwa Ibom mai zamanta a Okoita cikin Karamar Hukumar Ibiono Ibom, ta yanke hukuncin daurin shekara 28 a kurkuku kan wasu masu yi wa fasinjoji fashi a babur mai kafa uku su biyu.
Kotu ta kama wadanda lamarin ya shafa da laifin yi wa fasinja fashi a lokacin da yake kokarin shiga babur din a Hanyar Okokon Etuk da ke Uyo, babban birnin jihar.
- Kotu ta ci tarar ‘yan sanda N10m kan tsare dan kasuwa a Anambra
- Dogo Gide na neman N100m kan Daliban FGC Birnin Yauri
A nan ne suka kwace masa kwamfuta kirar Lenovo da waya kirar Gionee M5, ranar 7 ga Agusta, 2016.
Yayin shari’ar, Alkalin kotun, Mai Shari’a Okon Okon ya yanke wa ‘yan fashin zama kurku na shekara 21 kan aikata fashi, sannan 7 kan laifin hadin baki.
Alkalin ya kama wadanda ake karar da laifuka biyu daga cikin laifuka ukun da ake tuhumarsu, wato fashi da makami da hadin baki da ta’ammali da kungiyar asiri.
Sai dai ya wanke su daga zargin ta’ammali da kungiyar asiri duk da masu gabatar da karar sun bukaci kotun ta hukunta su a kan haka.
“Babu inda doka ta ce a hukunta mutum don ya yi ikirarin aikata laifi a wajen ‘yan sanda,” in ji Alkakin.