Tun bayan da aka zabi Sanata Ahmad Lawan Shugaban Majalisar Dattawa a majalisa ta tara ranar 11 ga Yunin da ya gabata, duk inda ya samu dama yakan nanata kudirin sabuwar majalisar mai rinjayen ’ya’yan Jam’iyyar APC da take da mulki a gwamnatin tsakiya, na ba da cikakken hadin kai da goyon baya da yin aiki tare da Bangaren Zartaswa na gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yadda za a gudu tare a tsira tare don gwamnatin APC ta samu cika alkawuran da ta yi wa talakawan kasar nan ta yadda za su gani a kasa, su samu saukin kuncin rayuwar da ake ciki.
An yi ta samun takun-saka a tsakanin Bangaren Zartarwa da na Majalisa a Majalisa ta Takwas da ta shude, duk da cewa Jam’iyyar APC ke da rinjaye a majalisun biyu a wancan lokaci.
An yi ta zargin cewa rashin samun hadin kan majalisun da bangaren zartarwar, ya yi ta kawo tarnaki da koma-baya sosai a tafiyar da harkokin Gwamnatin Tarayya ta Shugaba Muhammadu Buhari a zangon mulkinsa na farko, musamman batun amincewa da kasafin kudin shekara-shekara. Kasafin da a kai kasa ta dogara kacokan a dukkan abubuwan da za ta yi, walau tafiyar da ayyukan yau da kullum na gwamnati, ko na raya kasa, kamar gina hanyoyin mota da na jiragen kasa ko samar da ruwan sha ko kiwon lafiya ko ilimi da makamantansu.
Sau tari majalisun dokokin sun sha dora jinkirin da akan samu na wata shida zuwa bakwai kan kasa amincewa da kasafin kudin ga gazawar bangaren zartarwa ya mika musu daftarin kasafin kudin a kan lokaci, (wato cikin watan Satumba zuwa Oktoba), abin da sukan ce lokuta da dama sai a kusan karshen watan Nuwamba zuwa farkon Disamba, Bangaren Zartarwar kan gabatar musu dafatarin kasafin kudin.
Bayan jinkirin zartar da kasafin kudin kowace shekara da aka rika zargin majalisun na takwas, an kuma zargi majalisun biyu, musamman ta dattawa da jan kafa ko yin kememe wajen amincewa da bukatun da Bangaren Zartarwa kan mika mata, don neman amincewarta.
Alal misali har wa’adin Majalisar Dattawa ta Takwas ya kare, ta ki ta amince da nadin Alhaji Ibrahim Magu a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), duk da yadda Bangaren Zartarwar ya rika mika sunansa don neman amincewarta. Kazalika akwai dokoki da dama da har majalisun biyu suka kammala wa’adinsu da ake kiki-kaka a kansu tsakanin bangarorin biyu, misali, dokar harkokin man fetur din kasar nan.
Majalisun dokokin biyu sun ta kare kansu a kan dukkan zarge-zargen rashin bayar da hadin kai ga Bangaren Zartarwar.
Haka dai aka yi ta wancan zaman-doya da manja a tsakanin bangarorin biyu, kowa na jin shi ke kan daidai, alhali a gefe daya talakawan kasa suna ci gaba da zama cikin kuncin rayuwa da rashin tsaro da rashin ayyukan yi da uwa uba talauci. A haka har Allah Ya raba doki da kaska, ta yadda wadansu daga cikin wadanda suka rika kawo wancan tarnaki Allah bai sa sun sake samun nasarar dawowa majalisun ba. Wadanda kuma Allah Ya rabauta da dawowarsu, sun dawo a kan ba su da madafun ikon da suke da su a da.
A bisa ga yadda yake ta nanata tabbacin ba da hadin kai, na yin aiki tare da Bangaren Zartarwa, Sanata Ahmad Lawan ya fara nuna wa duniya cewa da gaske suke. Misali, bayan matsin lambar da aka yi ta yi wa Shugaba Muhammadu Buhari, na sai ya fito da jerin sunayen sababbin ministocinsa ya mika wa Majalisar Dattawa don neman amincewarta, bayan wata biyu, a wannan karo sabanin wata shida da ya dauka a zangonsa na farko bai fito da sunayen ministocin ba, Shugaban Kasar ya mika wa majalisar sunayen mutum 43 da yake so su zama ministoci a karshen watan Yulin da ya gabata. Majalisar Dattawan ta kuma jinkirta hutunta na shekara ta dukufa ba dare ba rana cikin zaman yini biyar (har da ranakun da ba ta zama na Litinin da Juma’a), ta tantance sunayen sababbin ministocin. Ministocin da Shugaba Buhari ya rantsar a shekaranjiya Laraba, bayan mako uku da samun amincewar majalisar.
Kazalika dawowar Shugaban Majalisar Dattawan ke da wuya daga aikin Hajjin bana a ranar Alhamis din makon jiya Kakakinsa Mista Ola Awoniyi, ya fitar da sanarwar da ke cewa Sanata Ahmad Lawan ya sake nanata kiransa ga Bangaren Zartarwa da su yi kokari su kasance a tare bisa ga tsarin aiki, ta yadda za a iya kauce wa rudanin da aka saba samu na jinkirin amincewa da kasafin kudi.
Sanarwar ta ce muddin majalisun dokokin na kasa za su samu daftarin kasafin kudin shekara mai zuwa a karshen watan gobe (Satumba), to ba makawa Majalisun za su iya aikin tantance daftarin cikin watan Oktoba zuwa Nuwamba, ta yadda za su iya kare komai kafin su tafi hutun Kirsimeti a watan Disamba. Hakan zai ba da dama a fara aiki da kasafin kudin a ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara.
A ziyarar Barka da Sallah da Shugaban Majalisar Dattawan ya jagoranci wadansu sanatoci da suka kai wa Shugaba Buhari a mahaifarsa garin Daura a ranar Juma’ar da ta gabata, Shugaban Majalisar ya fada wa manema labarai cewa za su tsaya a kan aikinsu na sa ido da bibiyar ayyukan Bangaren Zartarwa kamar yadda doka ta tanada. Hikimar haka inji Sanata Ahmad Lawan, ba ta wuce tabbatar da cewa kowa na yin aikin da aka dora masa ba, ta yadda da haka ne kawai za a iya kai mataki na gaba (Nes Lebul) kudirin wannan gwamnati ta Shugaba Buhari.
Mai karatu abin da nake so ka fahimta shi ne a wannan zangon mulki na biyu kuma na karshe ga Shugaba Muhammadu Buhari tun tafiya ba ta yi nisa ba, yanzu Shugaba Buhari da jam’iyyarsu ta APC suna da amintattun abokan aiki, sabanin wancan zango da wadansu suka yi wa jam’iyyar shigar burtu, daga bisani suka rika tadiye tafiyarta don tasu biyan bukatar. Al’amarin da ya zama hanzarin da Shugaba Buhari da gwamnatinsa da jam’iyyarsa ta APC suka rika bayarwa na kasa samun sukunin cika alkawurran da suka yi wa talakawan kasar nan na inganta rayuwarsu ta fannin tsaro da samar da ayyukan yi da ababen jin dadin rayuwa da sauran romon dimokuradiyya.
Da wannan samun hadin ko a iya cewa a wannan karon talakawa musamman na Arewacin kasar nan za su gani a kasa, “Wai an ce da kare ana biki a gidansu.