“Wannan na daga cikin abin da yake daure man kai, tare da ba ni mamaki a duk lokacin da na ji an furta wannan kalmar, Na Kiran Matasa da Sunan shugabanni gobe.
Ba komai yake sanya ni mamaki ba, da daure mani kai, a duk lokacin da na ji an furta wannan kalmar a wuraren tarukka, da makaloli, face, Irin halin da na ga ‘yan uwa na matasa ke ciki a wannan lokaci!.
Kamar yadda masana suka bayyana kalmar matasa, ga wadanda suke da shekaru daga 15 zuwa 40, wanda wannan yake nuna mana cewa, ke nan duk wanda ke da shekaru 15 zuwa 40, matashi ne.
“To Amma sai dai Kash! Ba komai ya sa na fadi haka ba, face irin yadda mafi akasarin masu shekaru 15 zuwa 40, su ne masu jini a jika, wadanda karfin su, yana karuwa, hankalinsa yana saituwa, tunaninsa yana fadaduwa, aikinsu yana kyautatuwa.
To, Amma duk da wannan za ka ga, galibin matasa masu shekarun da na zayyana, su ne ke zaune a cikin kunci da rashin ayukkan yi, uwa uba za ka ga kashi 99 cikin 100 na wadanda ke ta’ammali da miyagun kwayoyi za ka samu matasa ne. Wannan al’amari kan jefa rayuwar su cikin da na sani, wanda masu iya magana kan ce keya ce!
Ba komai ke janyo hakan ba, face talauci da ya yi wa matasan kaka gida, da kuma rashin ayukkan yi, domin galibi wadanda ke ta’ammali da miyagun kwayoyin za ka same su sun yi karatun a manyan-manyan makarantu na gaba da sakandare, har sun mallaki shaidar malanta ta, N.C.E, ko Diploma, wasun su ma har da babbar takardar kammala jami’a watau, Digiri`.
Amma Saboda rashin ayukkan yi da kuma mutuwar zuciya, ke jefa su aikata munanan laifuka. Ta yaya za a magance matsalar?
Hanyoyin magance matsalar abu ne mai sauki. Idan har gwamnatocin mu, kama daga na kananan hukumomi, zuwa jiha da ma Gwamnatin Tarayya suka yi Niyar magance matsalar!
Kamar yadda Hausawa, ko masu iya magana kan ce, idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai, tabbas haka ne. Doman kuwa a halin da muke ciki a Najeriya, an bayyana matasa a matsayin wadanda suka fi yawa a cikin kasar.
“To Tabbas magance matsalar 100 bisa 100, abu ne mai wuya, sai dai akwai hanyoyi masu dimbin yawan gaske, da za a iya magance matsalar rashin ayukkan yi ga matasa. Idan har gwamnatocin jihohi, da na kasa suka kudiri anniyar aiwatar da hakan!
‘Tun ran gini, tun ran zane,’ wannan ita ce babbar hanyar da za a iya bi, domin fara maganin matsalar daga matakin makarantun Firamare, da muke da su a kasar nan.
Ya zama Tilas idan Har gwamnati na son magance matsalar ta soma daga matakin farko, watau a makarantunan Firamare.
hanyar da za’a bi kuwa itace; Na kirkiro da wani darasi, da zai koyar da yara masu tasowa da ke makarantunnan, Dabarun koyon sana’o’in hannu, ko kafa sana’a domin dogaro da kai, a mataki na Farko ke nan.
A makarantunan sakandare kuwa, dama ana koyar da Fannin Kasuwanci, (Business) a Turance, sai a yi amfani da darasin, wajen koyar da dalibai dabarun dogaro da kai, tare da koyar da su sana’o’in hannu, kamar dinki da kafinta da injiniyanci, noma; kiwo, da makamantansu
A manyan makarantu dama a wasu makarantun ana koyar da darasin koyar da sana’o’i (Enterpreneuship), watau dabarun kirkiro da kasuwanci, ko rungumar kasuwanci komai kankantarsa, dama wannan darasin yana koyar da harkar dogaro da kai, da kuma kafa sana’o’i. A yi amfani da wannan damar wajen koyar da su zahirin sana’o’in da yin su a aikace (Practical).
Na yi Imani idan aka aiwatar da wannan, za ka samu galibin matasa sun kammala karatunsu, amma ba tare da sha’awar, aikin gwamnati ba. Doman dama an horar da su dabarun dogaro da kai, da kuma maganin zaman kashe wando.
“A gefen wadanda suka kammala karatunsu, da kuma wadanda ke a yankunan karkara a fito da shiri, da kowace karamar hukuma za ta koyar da matasan kowane gari, sana’o’in hannu, musamman sana’o’in gargajiya, tare da ba su jari bayan kammala horarwar. Idan aka yi wannan, za ka samu matasa, sun cimma burinsu na kasancewa shugabannin gobe.
Akwai mutane da dama, da kasuwanci ya habaka su, suka shahara da dubban jama’a ke ci ta hanyar su. To idan a ka bi wannan matasa ba ma za su yi sha’awar aikin gwamnati ba, bare fadawa cikin mummunar hanya, da kuma kauce wa ta’ammali da miyagun kwayoyi, da wasu ke fakewa da rashin aikin yi. Kuma wannan zai ba su damar amsa, kalmar da ake kiransu, da ita na matasa su ne shugabannin gobe.”.
Allah ya taimaki matasan kasata Najeriya, ya kuma Basu ikon kauce wa fadawa cikin munanan hanyoyi.
Dankaduna Amanawa. 09035522212. [email protected]
Ko matasa ne shugabannin gobe?
“Wannan na daga cikin abin da yake daure man kai, tare da ba ni mamaki a duk lokacin da na ji an furta wannan kalmar,…