Ina kuke samari ’yan lalle? Kuna ina ’yan matan zamani, adon gari? Ku zo ga wata tsaraba mai gwabi da FDK ya samo maku, daga taskar Nasir I. Mahuta.
Samari masu kankanba da hakilon wuce makadi da rawa a yayin nuna wa budurwa feleken soyayyar zamani, ya kamata ku karkade kunnuwanku ku saurari wannan tsokacin. Ina nufin samari da ’yan mata da suke ta’allaka soyayya da zinace-zinace, wadanda ke ganin cewa wai duk soyayyar da ba a surka ta da badalar zina ba, to ba ta kai soyayya ba, kaico.
Baya ga nafsoshin Alkur’ani da hadisi da suka haramta zina, to a wannan zamanin ma an samu tabbaci munin ta daga malaman kimiyya. Masana sun gano irin munin da ke tattare da zina da mazinata, sun gano dalilin da ya sanya Allah Ya haramta ta ga halittarSa.
Bincike ya nuna cewa duk lokacin da namiji ya sadu da mace, kwayoyin halittarsa na zama a jikin macen har abada.
Binciken wanda aka gudanar a Jami’ar Seattle da ke kasar Amurka ya tabbatar da cewa, yanzu an gano dalilin da ya sa Allah Ya haramta zina.
Dalilin kuwa shi ne, a duk lokacin da namiji ya sadu da mace wasu daga kwayoyin halittarsa suna yin hijira daga jikinsa zuwa jikin macen ta hanyar maniyyi. Hakan na nufin yawan saduwar da namiji zai yi da mace, to yawan kwayoyin halittarsa da za su zauna a jikin macen. Idan mace ta sadu da maza da yawa, dukkanin kwayoyin halittarsu suna zama a cikinta, sannan za su hadu a cikin kwayayen haihuwarta.
Binciken ya sake tabbatar da cewa, macen da ta sadu da mijin da ba nata ba, watau wanda ba aure suka yi ba, to ko ta haihu da mijinta sai kwayoyin halittar wanda ta sadu da shi din nan ya gauraya da na mijinta a jikin dan da ta haifa.
Saboda haka akwai bukatar mutane su sani akwai hadari babba tattare da saduwa kafin aure. Wannan ya kara nuna mana cewa ba wayewa ba ce ga samari da ’yan mata su ce za su sadu da juna kafin aure da sunan soyayya.
Binciken masanan ya kara tabbatar da cewa idan mace ta sadu da namiji to jikinta zai ginu da wani sashi na jikinsa, sannan hatta dabi’un ruhinta zai gauraye da na namijin da ta sadu da shi. Musamman idan mace ta sadu da maza da yawa, to tabbas za ta rayu da wani bangare na kwayoyin halittun mazaje da yawa a jikinta, haka ma dan da za ta haifa.
Mace na iya canjawa daga yanayin halittarta da zaran ta sadu da namiji saboda kwayoyin halittarsa zai gauraye da nata, ta kuma rayu da su a jikinta.
Binciken ya sake tabbatar da cewa duk miji da matan da suka dade suna tare, karshe za su koma suna kama da juna saboda gaurayewar kwayoyin halittarsu, sakamakon saduwa da juna yau da kullum da suke yi a rayuwarsu ta aure.
Kamar yadda binciken ya sake nunawa, kwayoyin halitta ne suke yin hijira daga jikin namiji zuwa jikin mace yayin saduwa, domin kuwa maniyyin namiji na dauke da kwayoyin halitta a cikinsa.
Da zarar maniyyin ya shiga jikin mace, yana gangarawa ne zuwa cikin mahaifarta kuma wani adadi na maniyyin zai manne a jikin namanta ta rayu da shi har abada.
Don haka, maganin a yi to kar a fara, masoya maza da mata, ku rika hakurewa da soyayyar zamani, kada ku sake ku aikata zina, ku hakura sai kun yi aure da juna sannan sai ku raya sunnar Manzon Allah (saw) yadda ya dace, yadda soyayyarku za ta zama mai tsarki.