Daidai misalin karfe tara da rabi na safe Binta ta yi sallama gidan su Saratu. Ta zo ne da nufin taimaka mata, domin su samu hanyar da za su magance matsalar da take damunta. Sun shirya cewa za su je Jami’ar Bayero, domin tunkarar Malam dandaula, wanda Saratu ta yi zargin ya yaudare ta, ya yi mata ciki. A ganawar da za su yi da shi, sun amince cewa za su bullo masa ta bayan gida, idan ya ki saurarensu.
Koda ta shiga dakin Saratu, ta same ta tana shafa, kasancewar ba ta dade da fitowa daga wanka ba. Bayan sun gaisa, Binta ta samu wuri ta zauna. Zamanta ke da wuya, abin kamar arashi sai aka dawo da wutar lantarki. dakin ya yi fayau da haske, kasancewar da ma ba a kashe gulab din dakin ba jiya da dare. Haka ma fanka ta fara wurga yatsunta da karfi, tana hura iska kowace kusurwa. Akwatin talabijin da ke girke a kuryar gabashin dakin, shi ma sai ya fara ruri, kasancewar ba a kashe shi ba a lokacin da aka dauke wuta.
Duk abubuwan nan da dawowar wutar lantarki ta haddasa, babu abin da ya fi daukar hankalin kawayen nan biyu kamar talabijin, domin kuwa wakar Barmani Coge ce mai taken ‘Ahayye Sama Ruwa kasa Ruwa’ take fesowa da karfin gaske, har sai da Binta ta dauki rimot ta rage karar.
“Ahayye sama ruwa kasa ruwa…Ladi ruwa-ruwa yana can kwance… sama ruwa kasa ruwa.”
Binta ce ta dage tana bibiyar wakar, a yayin da Barmani ke rera ta, karar kidan kwarya na tashi. A lokaci guda kuma tana karkada kirji, duk da cewa a zaune take.
Wakar Coge ba ta wuce minti biyu ba sai aka cire ta, aka maye gurbinta da labarun duniya. Wannan bai shalli kawayen biyu ba, kawai sai suka ci gaba da sharhin wakar nan.
“kawata, anya ba saboda ke aka sako wakar nan ba?” Inji Binta.
“Kamar yaya saboda ni, ban gane ba.” Saratu ta waigo ta kalli kawarta, yayin da take taje tsefaffen gashin kanta da wani dogon kumbi.
“Haka ne mana, ga shi za mu je wajen…ko kin mance da lokacin da kuka bararraje cikin ruwan sama da na kasa?” Ta kyalkyace da dariya.
“Wallahi ba ni son wulakanci!” Saratu ta tabune baki, a lokaci guda ta wurga mata kumbin da ke hannunta. A daidai lokacin kuma sai hankalinsu ya koma kan talabijin, kasancewar an ambata wani kanun labari da ya sanya duk suka dauki hankalinsu kacokan zuwa ga mai karanto labaran.
“Wata daliba A Jami’ar Bayero Ta Farke Makogwaron Malaminta…” Mai karanta labarin ya furta haka, a lokacin da ya gyara murya domin ci gaba da karanto gundarin labarin.
“A jiya ne da misalin karfe biyar na maraice, dalibai da malamai a Jami’ar Bayero suka tsinci kansu cikin jimamin yadda wata daliba ta farke makogwaron malaminta mai suna Malam dandaula Gagarau.” Gaba daya Saratu da Binta suka kara natsuwa kamar masu sauraren hudubar Juma’a.
“Malamin, wanda ke koyarwa a Tsangayar Ingilishi, ya gamu da wannan tsautsayi ne a hannun wata dalibarsa, Titi Gagara, wacce a yanzu haka take tsare a ofishin ’yan sanda. Malamin ya mutu a daidai lokacin da aka isa da shi asibiti, a sakamakon abin da likitoci suka ce, zubewar jininsa gaba daya.” Mai karanta labaran ya ci gaba da labarinsa, a yayin da kuma aka bijiro da hotunan gawar Malam dandaula da na dalibarsa Titi cikin ankwa, a lokacin da wata jami’ar ’yar sanda take yi mata rakiya.
Mai labarin ya ci gaba da bayyana yadda dalibar ta amsa laifinta. A daidai lokacin ne kuma aka nuno Titi tana magana da ’yan jarida, tana bayyana dalilinta na daukar matakin halaka malaminta.
Za mu ci gaba