✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kisan Ummita: Ba ni da laifi —Dan China

An sake gurfanar da dan kasar Chinan nan da ake zargi da kisan matashiya ’yar Kano.

Geng Quangron, dan kasar Chinan nan da ake tuhuma da kisan matashiyar budurwarsa  ’yar Kano, Ummulkusum Sani Buhari ya musanta aikata laifin.

Mista Geng ya bayyana hakan ne a gaban Babbar kotun Jihar Kano mai lamba 17 da ke Miller Road, yayin da kotun ta ci gaba da sauraren karar da Gwamantin Jihar Kano ta shigar tana zargin sa da kisan Ummulkusum.

Ana dai zargin Mista Geng da kisan Ummulkusum Buhari, wacce ta kasance budurwa a gare shi, inda ya shiga har cikin gidansu da ke unguwar Janbulo ya caccaka mata wuka, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarta.

A baya ana sami tsaikon sauraren shari’ar sakamakon rashin mai fassara ga wanda ake zargi, duba da cewa yana daga cikin hakkinsa a yi masa sharia da harshen da ya fi fahimta.

Sai dai a zaman na ranar Alhamis, mai gabatar da kara, Kwamishinan Sharia na Jihar Kano, Barista Musa A. Lawan ya gabatar wa kotun wanda zai yi aikin fassarar wanda kuma dan asalin kasar China ne mai suna Mista Guo Cumru.

Barista Musa Lawan ya shaida wa kotun cewa Ofishin Jakadancin Kasar China da ke Najeriya ne ya bayar da wanda zai yi aikin fassarar.

Daga nan Mai gabatar da kara ya karanta takardar karar inda ya bayyana cewa, “A ranar 16 ga watan Satumba, kai Mista Geng da ke zaune a rukunin gidajen da ke unguwar Railway a Jihar Kano ka je wani gida a unguwar Janbulo a Jihar Kano inda ka kashe wata budurwa mai suna Ummulkusum Sani Buhari ta hanyar caccaka mata wuka a wurare daban-daban na jikinta.

“Laifin da ake zargin ka da aikatawa dai ya saba da sashe na 221 a cikin Kundin Pinal Kod.”

Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake zargin sa da shi.

Mai gabatar da kara ya nemi kotun da ta daga shari’ar zuwa ranar 14 zuwa 16 ga watan Nuwamba don su gabatar da shaidunsu.

Sai dai lauyan wanda ake tuhuma Barista Muhamamd Balarabe Danazumi bai amince da wannan ranaku ba, inda ya shaida wa kotu cewa ranakun ba su yi masa daidai ba.

Sai dai mai gabatar da kara ya roki kotun da ta yi la’akari da cewa mai yin fassarar yana zuwa ne daga Abuja.

Alkalin kotun, Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji, ya dage shari’ar zuwa ranar 16 da 17 da 18 ga watan nuwamba, 2022