✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kisan Soleimani: Yadda Amurka ta daga hankalin duniya

Kisan da basar Amurka ta yi wa Babban Kwamndan Sojin Juyin Juya-Hali na basar Iran Janar Bassem Solaimani ya daga hankalin duniya, inda ake fargabar…

Kisan da basar Amurka ta yi wa Babban Kwamndan Sojin Juyin Juya-Hali na basar Iran Janar Bassem Solaimani ya daga hankalin duniya, inda ake fargabar barkewar mummunan yabi a Gabas ta Tsakiya.

Tuni wadansu suka fara  nuna fargabar cewa yabin da ka iya barkewa yana iya zama Yabin Duniya na Uku, da zai iya shafar sassan duniya.

A shekaranjiya Laraba aka wayi gari da labarin cewa basar Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami a kan wasu sanasanonin Amurka da ke Irabi a wani martani kan kisan Janar Soleimani da Amurka ta yi a makon jiya. Ministan Harkokin Wajen Iran, Mohammad Jabad Zarif ne ya fitar da sanarwar haka a shafinsa na Twitter, yana cewa harin na kariyar kai ne tare da nesanta harin da nufin bara dagula al’amura domin aukawa cikin yabi.

Me ya faru ne?

Kwana daya bayan kammala jana’izar Jana Bassem Soleimani, a talatainin daren Laraba (misalin barfe 12:30 agogon GMT) Rundunar Sojin Iran ta mayar da martani na farko kan basar Amurka, ta hanyar harba rokoki fiye da 12 a kan sansanonin basar biyu da ke cikin Irabi. Wasu daga cikin makamai masu linzamin da Iran ta harba sun fada ne a kan barikin soji na Ainal-Assad mai tazarar kilomita 230 a yammacin birnin Bagadaza, barikin da Donald Trump ya ziyarta don ganawa da dakarun Amurka a watan Disamban 2018, yayin da sauran makaman suka fada a barikin sojin Erbil da ke gabashin basar.

Sanarwar da ta fitar jim kadan bayan hare-haren, rundunar kare juyin juya-halin Musulunci ta basar ta Iran ta ce ta shirya tsaf domin yin fito-na-fito da Amurka, tare da yin barazanar kai irin wadannan hare-hare a kan basar Isra’ila, yayin da ta ce duk wata basa da Amurka za ta yi amfani da ita don kai mata farmaki ita ma za ta iya fuskantar mummunan martani.

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta tabbatar da kai hare-haren, inda ta ce yanzu haka ana ci gaba da tantance irin illolin da suka haddasa.  Lura da halin da ake ciki, Amurka ta bubaci jiragenta masu jigilar fasinjoji su baurace wa sararin samaniyar yankin Gabas-ta-Tsakiya baki daya.

Kasuwannin hannayen jari a basashen Asiya sun bude a cikin yanayi na firgita, yayin da tuni farashin man fetur ya tashi da aballa kashi 4.5 a yankin Asiya.

Barnar da harin ya yi

Babu bayanai a hukumance kan irin barnar da hare-haren suka haddasa. Dakarun Irabi sun ce harin bai hallaka musu ko soja daya ba. Basashen Jamus da  Poland da Norway da Denmark sun ce ko da sojansu guda bai hallaka ba, kuma babu wanda ya yi rauni sakamakon harin na Iran.  Gidan talabijin na Iran ya yi ikirarin aballa ‘Amurkawa ’yan ta’adda 80’ ne suka hallaka a harin da Iran ta kai da makamai masu linzami 15, ya kuma bara da cewa ba a iya kakkabo ko daya daga cikinsu ba. Ko da yake babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin na gidan talabijin din, Shugaban Amuka Donald Trump ya fadi a yammacin shekaranjiya cewa babi wanda ya rasa ransa a harin na Iran  kuma zai dauki matakin bara sanya wa basar takunkumin tattalin arziki.

Me ya sa aka kai harin?

Kafar labaran Iran ta ce harin na ramuwar gayya ne kan kisan Janar kuma Babban Kwamandanta Basem Soleimani da aka kashe a hari ta sama a Bagadaza, bisa umarnin Shugaba Donald Trump. Ita ma Rundunar Juyin Juya-Halin Iran ta ce harin na ramuwar gayya ce kan kisan Soleimani a ranar Juma’a

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta ce aballa sansani biyu aka kai wa hari a Irbil da Ain Al-Asad. Babu dai wani cikakken bayani game da hare-haren na Iran.

Mai magana da yawun fadar White House Stephanie Grisham ta fadi cikin wata sanarwa cewa, “Mun samu rahotannin hare-hare kan sansanonin Amurka a Irabi. An sanar da Shugaban Basa kuma muna sa ido kan lamarin tare da tuntubar ayarinsa na tsaron basa.”

Ministan Harkokin Wajen Iran Jabad Zarif ya ce Amurka ta bi ba shi bizar shiga basar domin halartar wani taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York. Kasancewar Amurka basar da hedkwatar Majalisar Dinkin Duniyar take kamata ya yi ta riba byale jami’an basa da basa suna halartar tarurrukan majalisar.  “Suna fargabar kada wani ya shiga Amurka ya bayyana gaskiyar al’amarin,” inji Zarif. Sai dai Ma’aikatar Wajen Amurkar ba ta ce uffan ba game da neman bizar da Zarif ya yi.

Mutum 50 sun rasu a turmutsitsin jana’izar Soleimani

Aballa mutum 50 ne suka rasu a turmutsitsi a Iran yayin da ’yan basar ke tururuwa zuwa wajen jana’izar Janar Soleimani da aka kashe a harin da Amurka ta kai, ranar Juma’a a filin jiragen saman Bagadaza.

Hukumomin basar ba su da takamaiman adadin mutanen da suka rasu a turmutsitsin, sai dai jami’an ko-ta-kwana sun tabbatar da mace-mace da dama. Rahotanni sun ce sama da mutum 100 sun raunata. An yi biyasin miliyoyin mutane ne suka taru a wajen jana’izarsa a mahaifarsa Kerman.

Wane ne Janar Basem Soleimani?

Janar Soleimani mai shekara 62, ya jagoranci sojojin Kurdawa da Amurka ta zarga da shirya kai hare-hare kai-tsaye ko ta hanyoyin da suke kusa da su – a cikin nahiyoyi biyar na duniya. Shugaba Donald Trump ne ya bayar da umarnin kai harin bayan wasu hare-hare na baya-bayan nan kan ofishin jakadancin Amurka a Irabi wanda aka dora wa mayaban da ke samun goyon bayan Iran.

Suna da shahara a Iran

Ana kallon Janar Soleimani tamkar gwarzo a Iran, yayin da wadansu ke bayyana shi a matsayin na biyu wajen barfin fada-a-ji bayan jagoran addini na basar, Ayatollah Khamenei. Ya fara shahara ne a baya-bayan nan inda yake jagorantar ayyuka domin yin suna da samun karbuwa a Iran, kuma ake bada rahoto game da shi a kafafen watsa labarai.

Yadda ya zama babban kwamanda

Janar Soleimani ya taso ne a gidan marasa barfi, sannan yana da barancin ilimin zamani.

Sai dai ya yi suna a cikin sojojin Juyin Juya -Halin, wadanda suka yi fice a Iran kuma an ruwaito su suka fi kusa da Jagoran Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei.

Ya yi suna a lokacin yabin da aka yi tsakanin Iran da Irabi a tsakanin 1980 zuwa 1988 daga nan kuma ya samu barin matsayi zuwa babban kwamanda. Bayan ya zamo jagoran dakarun Kurdawa a 1998, Soleimani ya yi bobarin fadada tasirin Iran a Gabas ta Tsakiya ta hanyar jagorantar hare-hare tare da samar da makamai ga bawayen Iran da kuma bunbasa mayaban da ke bai wa Iran goyon baya.

Janar Soleimani ya taimaka wa ’yan Shi’a da bungiyoyin Kurdawa a Irabi da ke yabi da marigayi Shugaba Saddam Hussein da wasu bugiyoyi a yankin ciki har da Bungiyar Hezbollah a Lebanon da Hamas a yankin Palasdinu. Bayan Amurka ta mamaye Irabi a 2003, Soleimani ya fara bai wa mayaba umarnin kai hare-hare kan dakarun Amurka da sansanin sojojin Amurka, lamarin da ya hallaka daruruwa. An ce ya samar da wata dabara ga Shugaban Syria, Bashar al-Assad domin mayar da martani kan tawayen da aka yi masa a shekarar 2011. Kuma tallafin da Iran da Rasha suka ba Assada ya sa lamura sun sauya kan ’yan tawayen abin da ya bai wa gwamnati damar bwace muhimman birane da yankuna.

A wasu lokutan an sha ganin Soleimani da kansa a jana’izar mutanen Iran da Syria da Irabi suka kashe. Yana kuma da tasiri a yabin da aka yi da Bungiyar IS a Irabi.

Iran ta taimaka wajen bada makamai da horar da dakaru abin da ya taimaka wajen samun galaba a kan IS amma da yawan ’yan Irabi na ganin kamar mulkin mallaka Iran din take yi musu.

Kashe shi da martanin ’yarsa

Amurka ta yi amfani da jirgi marar matubi wajen kai harin da ya kashe Janar Soleimani a ranar Juma’a a Irabi bayan Shugaba Trump ya bayar da umarnin a hallaka shi.

Zainab Soleimani ’yar marigayin, ta gargadi Amurka kan abin da zai biyo baya, tana mai bayyana Shugaba Donald Trump a matsayin mahaukaci, sannan ta ce “Kada ka zaci komai ya bare bayan shahadar mahaifina.”

Cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Tsaron Amurka ta ce Soleimani ya dade “yana bijiro da tsare-tsaren kai wa jakadun Amurka hari a Irabi da sauran sassan duniya. Janar Soleimani da dakarun Kurdawa su ne suka kashe daruruwan Amurkawa tare da raunata wadansu da dama,” kamar yadda sanarwar Amurka ta bayyana.

%d bloggers like this: