✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Sakkwato: Jama’a sun aike wa Buhari wasikar bacin rai

Mutane na yunkuri yi wa Buhari zanga-zanga kan kisan gillar da ’yan bindiga ke yi a Jihar Sakkwato

Jama’ar yankin Sabon Birni a Jihar Sakwkato sun aike wa Shugaba Muhammadu Buhari wasikar nuna fushinsu kan irin kisan gillar da ’yan ke musu kusan kullum a yankin.

Shugabannin Karamar Hukumar sun aike wa Buhari wasikar ce bayan ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 80 cikin dare daya a Jihar Sakkwato.

Kisan na biyu na zuwa ne bayan wasu ’yan bindiga sun tare wata mota a kauyen Gidan Bawa da ke jihar, inda suka kone fasinjoji sama da 40 kurmus.

Wasikar ta bayyana wa Buhari rakaicinsu kan irin kisan gillar da a ake yi musamman a yankunan Isa, Sabon Birni, Goronyo da kuma Karamar Hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara wadda ke makwabtaka da Jihar Sakkwato.

Shugabannin yankin sun ce ’yan ta’adda masu biyayya ga kasungurmin dan bindigar nan, Bello Turji, na kai farmaki kan al’ummomin yankunan, inda suke yi wa mata fyade baya ga lalata dukiyoyin jama’a.

A baya jama’ar Sabon Birnin sun taba rubuta wa Shugaba Buhari wasika domin shaida masa irin mawuyacin halin da suke fuskanta a yankinsu.

Takaicin kisan gillar ya sa fusatattun mutane da zargin Buhari da rashin katabus a kan lamarin, sai ma tafiya Jihar Legas da ya yi a ranar Alhamis, domin halartar taron kaddamar da littafi.

Tuni dai mutane a kafafen sada zumunta suka shiga kira da a yi zanga-zanga tare da neman wa shugaba Buhari ya sauka daga mulki kan rashin kawo karshen matsalar tsaro da ta damu wasu yankuna, musamman na Arewacin Najeriya.