Salam Edita ku ba ni dama da farko inyi Allah game da kisan kiyashin da a ke yi wa yan uwan mu Mmusulmi ’yan kabilar Rohingya a kasar Burma wato
Myammar, Hakan bai dace ba kuma keta dokar hakkin dan Adam ce.
Sannan ina so ku ba ni dama in yi kira ga kwamitin sulhu Majalisar dinkin Duniya, Ya hukunta kasar Burma akan take hakkin yan ta’adda tare da aikata kisan kiyashi, Kuma kotun du niya ta ICC Da ke da mazaune a birnin Hague ya kamata ta yi bincike na gaskiya don hukunta shugabanin rundunar sojan kasar da kuma saurin masu ruwa da tsaki a halaka yan Adam a kasar!
Ina so in yi kira ga kasashen Musulmi, Kamar su Saudiyya da katar da Irak. Da kuma UAE Ya kamata su yi koyi da shugaban kasar Turkiyya Rasif Tayif
Erdogan wajen tura wakilai a kasar Burma don tattaunawa da kasar da kuma neman dakatar da kisan kiyashi da kona gidajen Musulmi da ake yi a kasar,
Sannan ya kamata a kai wa masu gudun hijra a kasar Bangaladesh tallafin abinci da sutura da magunguna, Domin kula da su la’akari da halin da suka fada a ciki!
Duk mai bibiyar abin da ke faruwa a kasar yasan halin matsi da mutanen ke ciki, Maza da mata, Yara da manya babu abinci da sutura ga ruwan sama, Muddin kana kallon ba kasan lokacin da hawaye za su cika zubo daga idanun ka ba! Allah ya kawo mafita.
Daga Ibrahim Rabilu jihar Zamfara Najeriya 07064282182 [email protected].