✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan matafiya: An sanya dokar hana fita a Filato

Gwamnan ya ce an cafke mutum 20 da ake zargin na da hannu a kisan matafiyan.

Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana fita a wasu Kananan Hukumomi uku daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe.

Kananan Hukumomin da aka kakaba wa dokar  sun hada da Bassa, Jos ta Arewa da Jos ta Kudu.

  1. Dan Arewa ne kadai zai iya lashe wa PDP zabe a 2023 – Dokpesi
  2. An yi garkuwa da matafiya 15, an kashe wasu a Jos

Matakin hakan ya biyo bayan kashe wasu matafiya 25 tare da jikkatar wasu mutane da dama da aka ranar Asabar a Jos, babban birnin Jihar.

Gwamna Simon Lalong a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Dokta Makut Macham ya fitar, ya ce dokar hana fitar za ta fara tun daga ranar 14 ga watan Agusta.

“Na ba da umarnin sanya dokar hana fita a kananan hukumomin Jos ta Arewa, Bassa da Jos ta Kudu, wanda zata fara aiki daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe daga 14 ga Agusta 2021.

“Dokar hana fita za ta ci gaba da kasancewa, kwamitin tsaro zai ci gaba da bincike” in ji sanarwar.

Gwamnan ya yi gargadin sabawa umarnin, yana mai cewa jami’an tsaro za su dauki dukkan matakan kiyaye doka da oda a yankunan da abin ya shafa.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da sanya ido kan lamarin tare da daukar karin mataki idan ya zama dole, don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

Lalong ya kuma yi kira da a kwantar da hankula tare da yin kira ga mazauna yankin da su guji duk wani mataki ko maganganun da za su kara rura wutar lamarin, yana mai cewa hukumomin tsaro na gudanar da bincike kan harin.

“Zuwa yanzu, an cafke mutane 20 da ake zargi kuma hukumomin tsaro na gudanar da bincike don gano asalin lamarin,” in ji shi.

Ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu, da wadanda suka jikkata sakamakon mummunan abin da ya faru.