Marasa Rinjaye na Majalisa ya hawarci Gwamantin Tarayya ta sake dabarun yaki da Boko Haram da masu garkuwa da mutane a fadin Najeriya.
Kwamitin ya ce bai kamata kullum ana kashe mutane amma ba abin da Fadar Shugaban Kasa ke yi face Allah-wadai.
- Boko Haram ta yi wa manoma 43 yankan rago a Borno
- Harin sojojin sama ya kashe ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa
- Kisan Zabarmari: Tambuwal da Zulum za su yi aiki don gano mamata
- Yadda Zulum ya halarci jana’izar manoma 43 da aka yi wa yankan Rago
Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya ce yanzu lokaci ya yi na gwamnati ta dauki tsauraran matakai tare da yin nazarin dabarunta tunda na yanzu sun gaza matuka.
Kwamitin ya kuma nuna alhini tare da bacin rai game da kisan da aka yi wa manoman shinkafa a Jihar Borno.
Sanarwar kwamitin ta kara da cewa abun takaici ne a ce lokacin da ake sa ran yin girbin kayan abinci ya koma lokacin zaman makoki.
Sun kuma aike da sakon ta’aziyya ga gwamnatin Borno da iyalan wanda aka yi wa kisan gillar.