✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Kwamandan Soji ya jefa jama’a cikin damuwa

Birged din Sojn Atilare ta 33 da ke Bauchi ta fada cikin jimami da alhinin rashin daya daga cikin kwamandojinta Kanar Muhammad Barak. An wayi…

Birged din Sojn Atilare ta 33 da ke Bauchi ta fada cikin jimami da alhinin rashin daya daga cikin kwamandojinta Kanar Muhammad Barak.

An wayi garin ranar Litinin da ta gabata ce da labarin kisan Kwamandan, wanda ake kira da ‘Garrison Commander’ na birged din.

Wannan kisan ya tayar da hankalin jama’ar garin saboda tsoron abin da zai iya biyowa baya. Har yanzu dai ba a tabbatar da wadanda suka yi kisan ba.

Wannan abu da ya faru a hanyar Bauchi zuwa Jos a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da marigayin, wanda dan asalin Jihar Kano ne yake tukin babur din da ake kira Powerbike.

Kakakin Birged na 33, Manjo Yahaya Nasir Kabara ya tabbatar da kisan Kwamandan, sai dai bai yi wani karin haske a kai ba. “An kashe shi, Allah Ya jikansa. Ba wani karin bayani da za mu yi saboda abu ne mai bukatar bincike, muna kan bincike. Zan tuntube ku idan muka gano wani abu,” inji Manjo Yahaya Nasir Kabara.

Duk kokarin da manema labarai suka yi don jin wani cikakken bayani daga sojojin cewa suke yi yanzu sun je sun binne shi a Kano bayan da aka yi masa faretin girmamawa kuma ba wani abin da za su iya karawa a kai, illa dai Hedikwatar Tsaro ta Kasa za ta ba da sanarwa kan rasuwar tasa.

Wata majiya a barikin soji na Shadawanka da ke Bauchi ta ce ba hadari marigayin ya yi ba, illa iyaka babur dinsa ne ya lalace, lokacin da yake jiran yadda za a yi a gyara ko ya isa gida sai wadansu ’yan bidiga suka fito daga cikin daji suka yi masa harbi har guda uku a kafarsa da cikinsa da kuma kansa.

Rasuwar Kwamandan ta jawo jimami da alhini da kuma sanya al’ummar Jihar Bauchi suna cikin rudani, inda kowa ke fadin albarkacin bakinsa. Malam Muhammadu Mustafa Alkaleri ya ce “Rashin wannan babban jami’in soja ya girgiza ni matuka kuma wannan ya nuna cewa matsalar tsaro da ake ta fama da ita tana nan. Ya kamata gwamnati ta mike tsaye ta shawo kan lamarin. Idan ya zama ana kashe sojoji, ke nan ba wanda za a iya cewa ransa ya tsira.”

Ita kuwa Hajiya Rabi Jama’are cewa ta yi “Gaskiya rasuwar wannan Kwamanda babban rashi ne, muna ta’aziyya ga iyalansa da Rundunar Sojin Najeriya, muna kuma kira a gare su da su yi binciken kwakwaf irin wanda suka yi a yankin Filato bayan kisan gillar da aka yi wa marigayi Janar Alkali domin a gurfanar da wadanda suka yi kisan a gaban kotu.”

Tambayar da mutane ke ta yi ita ce, su wane ne suka kashe shi kuma wane dalili ya sa suka kashe shi? Cikakken bincike ne zai tabbatar da abin da ya faru.