✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan kiyashi a wata makaranta da ke Pakistan

A ranar Talatar makon jiya ne kungiyar Taliban ta kai wani mummunar hari a wata makaranta da ke birnin Peshawar a kasar Pakistan, wanda ya…

A ranar Talatar makon jiya ne kungiyar Taliban ta kai wani mummunar hari a wata makaranta da ke birnin Peshawar a kasar Pakistan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 149, kuma 132 daga cikinsu yara ne. Sakamakon munin harin, reshen kungiyar Taliban da ke Afghanistan ya nisanta kansa daga farmakin, inda ta bayyana alhininta da kuma bayyana  kisan mata da yara da wani abu da ya saba wa addinin Musulunci. Har ila yau, reshen kungiyar al-kaeda na Kudu-maso-Yammacin nahiyar Asiya, wanda ya lashi takofin yaki da mamayar Yammacin Duniya, ya fitar da wata sanarwa wadda ciki ta yi Allah-wadai da harin, inda ta ce ranta ya baci matuka sakamakon kisan kiyashin. Ko shakka babu harin wani babban tashin hankali ne da ya fada wa Bil’adama. Hakan kuma ya jefa  duniya baki daya cikin makoki.
A lokacin da maharan suka dira makarantar, wadda rundunar sojin kasar Pakistan take tafiyarwa, irin harbe-harbe da taka bama-baman da ya faru ya bazu zuwa duka fadin duniya, inda ya zama farmakin da fi kowane muni a tarihin kasar. Cikin wadanda suka rasa rayukansu har da malaman makarantar su 10. Hakazalika, sakamakon musayar wuta da jami’an tsaro ya sa ba ko da mutum guda daga cikin maharan da ya tsira.
Lamarin ya fara ne da safe, lokacin da mahara tara sanye da kaya irin na jami’an tsaro suka shiga makarantar daga  katangar baya, makarantar da ke da dalibai maza da mata da suka samma 2,500 kamar yadda wani babban jami’in tsaro ya bayyana.
Maharan sun jefa gurnade tare da harbi kan mai uwa da wabi. Ministan Yada Labarai na lardin Khyber-Paktunkhwa,  Mushtak Ghani, ya ce harbi a ka ne ya yi ajalin yawancin wadanda suka rasa rayukansu. Amma a lokacin da mai magana da  yawun reshen kungiyar Taliban da ke Pakistan wanda kuma aka fi sani da Tehreek-Taliban Pakistan (TTP)
ya ce  su ke da alhakin kai harin, kuma ya bayyana shi da harin daukar fansa ga sojoji da ke kai farmaki a Arewacin lardin Waziristan. Akan batun wadanda suka hara, ya ce sun kai farmakin ne saboda ’ya’yan sojoji ne ke karatu a makarantar kuma galibinsu suna fatan shiga aikin soja kamar iyayensu. Wanda hakan ke nufin suma a nan gaba za su yaki ’yan gwagwarmaya.
Sai dai a lokacin da dakarun Pakistan suke mayar da martani ga maharan, wasu daga cikin maharan sun kashe kansu, yayin da dakarun musamman suka kashe saura.
kungiyar Taliban ta ce tana fafutukar addini ne; sai dai kuma ba wani addini da yake umarnin kisan rayukan da ba su ji ba, ba su gani ba. Masu fafutukar suna fassara addinin Islama ne bisa ra’ayin da zai dace da munanan ayyukan da suke kaddamarwa. Sai dai wannan gurguwar fahimtar ta su ta saba wa koyarwar addini, saboda addinin Musulunci addini ne da ke daraja rai.
Idan suna tunanin an masu ba daidai ba, to fa ba ta yadda za a ce kisan kananan yara a makarantar da ke karkashin kulawar sojoji ya dace.
Kamar yadda kungiyar al-kaeda ta bayyana, idan har reshen kungiyar Taliban da ke Pakistan zai dau fansa, to kan sojoji ne, amma ba mata da kananan yara ba. Har ila yau, wannan farmakin ya tilasta wa gwamnatin Pakistan dakatar da afuwa ga masu laifukan da suka jibanci ta’addanci. Hakan ya sanya jim kadan bayan kai farmakin, aka aiwatar da hukunci kisa ga ’yan Taliban da ke tsare; kungiyar ta sha alwashin daukar fansa. Ita kuma gwamnatin ta zafafa farmakin da ta kai wa mambobin kungiyar. Firaministan kasar Nawaz Sharif ya gayyaci duka jam’iyyun kasar zuwa wani babban taro da zai lalubo dabarun yaki da kungiyar Taliban. Haren-haren kungiyar ya jawo mata bakin jini a duk fadin duniya kuma ya sanya ta a jerin kungiyoyin ’yan ta’adda. Har ila yau, ya dace gwamnatin ta dauki barazanar daukar fansar ba da wasa ba, san nan kuma ta kara kaimi.