Babban shehin Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bukaci gwamnati ta biya diyyar mabiyansa da aka karkashe a yankin Gada-Biyu na garin Jos na Jihar Filato a ranar Asabar.
Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya bukaci biyan diyyar daga Gwamnatin Jihar Filato ya kuma nemi a hukunta wadanda suka kashe almajiran nasa guda 30 tare da jikkata wasu da dama.
Latsa nan domin sauraren ‘Yadda sabuwar dokar man fetur za ta shafi rayuwarku’:
– An kashe karin mutum 7 bayan kisan matafiya a Jos
– Yadda muka tsallake rijiya da baya a harin Jos
Shehin malamin, wanda Shugaban Kasa ya yi wa ta’aziyya bisa wakilcin Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami, ya bayyana bukatar biyan diyya ga iyalan mamatan da kuma hukunta masu laifin ne a wata zantawa da Sashen Hausa na BBC ya yi da shi.
Sheikh Dahiru Bauchi ya kuma gargadi al’ummar Musulmi da su nisanci daukar doka a hannunsu da sunan daukar fansa a kan kisan matafiyan da aka yi.
Tun bayan faruwar lamarin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a kamo tare da hukunta wadanda suka yi wa matafiyan kisan gilla.
Tuni dai Gwamnatin Jihar Filato ta sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a garin Jos, ta kuma sanar da kama wasu mutum 20 bisa zargin su da hannu a kisan gillar da aka yi wa Fulanin.
Matafiyan na hanyarsu ta komawa Jihohin Ondo da Ekiti da kuma kasar Ghana ne bayan sun halarci taron bikin Sabuwar Shekarar Musulunci, inda suka ziyarci Sheikh Dahiru Bauchi a gidansa da ke garin Bauchi.
Isowarsu yankin Gada-Biyu da ke garin Jos ke da wuya aka yi tare motocinsu aka yi wa wasunsu kisan gilla, wasu kuma suka tsallake rijiya da baya.
Hukumomin ’yan sanda sun zargi ’yan kabilar Irigwe da ke yankin da kai harin, a yayin da kungiyar ’yan kabilar Irigwe ta kasa ta la’anci maharan.
Yankin ya yi fama da rikice-rikice a baya-bayan nan, inda aka yi ta kai hare-haren daukar fansa tsakanin ’yan kabilar ta Irigwe da Fulani.
Ita ma Kungiyar Tarayyar Mata Muslim ta Najeriya (FOMWAN), ta bayyana damuwarta kan kisan, wanda ta bayyana a matsayin abun kyama.
Shugabar FOMWAN ta Kasa, Hajiya Halimah Jibril wadda ta yi tir da harin ta bukaci gwamnati da ta gudanar da zuzzurfan bincike don gurfanar da wanda suka aikata laifin domin ya zama aizina ga wadanda za su yi yunkurin aikata irin hakan a nan gaba.
“FOMWAN ta yi bakin ciki da wannan mummunan laifi da aka aikata, don haka muna tuni a kan a gurfanar tare da hukunta wanda suka aikata laifin don zama izina ga wanda suka da tunani irin wannan,” inji ta.