Kungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze da ta ’yan awaren Biyafara (IPOB), sun caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Imo Hope Uzodimma, kan kalaman da suka yi dangane da kisan wasu ‘yan kasar Nijar takwas da kuma wasu jami’an tsaro a birnin Owerri.
An baya nan ne Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu, ya yi Allah wadai tare da kira ga al’ummar jihar da su fallasa wadanda ke da hannu a kishe-kashen.
- Nan da ’yan makonni za a magance matsalar tsaro a yankinmu —Wase
- Duk wanda ba ya kaunar Jihar Ribas kar ya sa rai da kuri’unmu —Wike
Kazalika, shi ma Shugaba Buhari ya yi kira ga al’umma da shugabannin addini da su nuna wa jama’a illar kashe-kashe tare da kare addini da kuma kyawawan al’adun kasa.
Sai dai a martanin da kungiyar Ohanaeze ta mayar wa Buhari cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce Buharin ya daina magana kamar a Kudu maso Gabas kadai irin haka ke faruwa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito Sakataren kungiyar, Dokta Chiedozie Ogbonnia, ya ce a bayyane yake an fi samun kashe-kashe da ayyukan ta’addanci a yankin Arewar da Buhari ya fito fiye da Kudu maso Gabas.
A nasu bangaren, ‘yan awaren Biyafar (IPOB), sun musanta zargin cewa suna da hannu a kisan ‘yan Nijar din da jami’an tsaron a Owerri.
Cikin sanarwar da ta fitar ta hannun sakataren yada labaranta, IPOB ta ce tana mamakin yadda Fadar Shugaban Kasa kan gaggauta yin tsokaci a duk lokacin da matsalar tsaro ta rutsa da ‘yan Arewa.
IPOB ta kuma kalubalanci Fadar Shugaban Kasa da ta bayyana adadin lokutan da ta bai wa shugabannin Arewa umarnin fito da wadanda suka kashe ‘yan Kudu mazauna Arewa.
A kan haka ne IPOB take cewa, laifin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Imo ya kamata a gani dangane da kashe-kashen da ke faruwa a jihar amma ba IPOB da sauransu ba.