Daruruwan mutane ne suka fita zanga- zanga a wasu manyan biranen kasar Sudan a bisa kisan wasu Hausawa da aka yi a ciki da kuma kauyukan garin Damazin da ke jihar Blue Nile A ranar Litinin
Masu zanga-zangar na neman gwamnati ta zakulo, tare da hukunta duk wadanda suke da hannu a kan kisan mutanen da suka ce na babu gaira babu dalili ne.
- Kowanne dan Najeriya yanzu yana da hannun jari a NNPC – Mele Kyari
- Shugaban Amurka ya kamu da COVID-19 duk da an yi masa rigakafinta
Matasa maza da mata ne suka fantsama mayan titunan Khartoum babban birnin kasar dauke da kwalaye masu rubuce-rubucen la’antar abin da ya faru tare da kiran gwamnati da ta dauki mataki.
A jawabinsa ga masu zanga-zangar, Gwamnan jihar ta Blue Nile inda abin ya faru, ya yi kira ga matasan da su kwantar da hankalinsu kar kuma su dauki doka a hannunsu.
Uztaz Tidjani Musa shugaban al’ummar Hausawa na kasar a jawabinsa a gaban Gwamnan, ya ce Hausawa mutane ne masu son zaman lafiya shi ya sa ba su dauki doka a hannunsu ba.
Ya ce kuma ce lallai ne gwamnati ta dauki matakin da yace.
Ana zargin ’yan kabilar Marti tare da hadin bakin wasu kabilu na yankin da aikata kisan tare da kona dukiyoyin Hausawa da Fulani da kuma Barebari da ke zaune a yankin.
A cewar wasu rahotanni, rikicin ya samo asali ne daga wani yunkurin da Hausawa suka yi na kafa masarauta wacce za ta kula da al’amuransu.
’Yan kabilar ta Marti suka kalli lamarin a matsayin barazana a garesu musamman ta fuskar filin noma.
Duk da cewa kabilun Hausawa da Fulani, da Barebari an haifi iyayensu da kakanni yankin, kabiliun wurin na ci gaba da kallonsu a matsayin baki.