✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kisan Harira: ’Yan IPOB za su dandana kudarsu — Buhari

Ya kuma gargadi masu yada hotunan kisan a shafukan sada zumunta

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan da ’yan haramtacciyar kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB suka yi wata ’yar Arewa mai suna Harira da ’ya’yanta su hudu a Jihar Anambra.

Shugaban ya bayyana kisan nata da ma na sauran mutane da kungiyar ke ci gaba da yi a yankin a matsayin dabbanci, inda ya ce za su dandana kudarsu.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shi, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Laraba, Buhari ya gargadesu cewa su jira tsattsauran mataki daga jami’an tsaro.

Buhari ya kuma yi gargadi a kan daukar kowanne irin mataki na ramuwar gayya daga kowane bangare na kasar.

Ya ce yanzu haka, jami’an tsaro na bincike kan sahihanci da gaskiyar hotuna masu tayar da hankali da ake yadawa a kan kisan.

Sanarwar ta kuma gargadi ’yan Najeriya da su guji gaggawar yanke hukunci ko daukar duk wani matakin da zai dada dagula al’amura, inda ya ce kamata ya yi a kyale doka ta yi aikinta.

Buhari ya kuma gargadi jama’a kan ci gaba da yada hotunan musamman a kafafen sada zumunta domin su ba masu yunkurin raba kan kasa kunya.