Kisan gillar da aka yi wa karamar yarinyar nan mai shekara biyar, Hanifa Abubakar, wadda mai makarantarsu ya sace ya kuma kashe ta, ya sauya yanayin zuwa makaranta da kuma alaka tsakanin malamai da dalibai da kuma tsakanin iyayen dalibai da makarantu a Jihar Kano.
Tun bayan kisan gillar da aka yi wa Hanifa, iyayen dalibai suka shiga cikin damuwa, ta yadda suka koma zuwa makarantu tun kafin lokacin tashi domin daukar ’ya’yansu da zarar an kada kararrawar tashi.
- Pantami ya ziyarci iyayen Hanifa a Kano
- A shirye nake in sa hannu a hukuncin kisa kan makashin Hanifa —Ganduje
Tsakanin dalibai da malamai kuma an koma yin nesa-nesa da juna, inda malamai ke tsoron kusantar dalibai saboda gudun zargi, su kuma dalibai suna kaffa-kaffa saboda tsoron kar a yi garkuwa da su.
Bayan labarin kisan Hanifa, iyaye kuma, sun bukaci makarantu da su samar da takardar shaidar shiga da kuma daukar yara a makaranta a wani yunkuri na tabbatar da tsaron lafiyar ’ya’yan nasu a makarantu.
Bugu da kari, yanayin zuwan dalibai makaranta ya sauya, yanzu hatta yaran da a baya suke zuwa makaranta da kansu, an koma kai su, iyaye kuma kan je tun kafin lokacin tashi domin daukar ’ya’yansu da kuma tabbatar da amincinsu a makarantun.
Kisan Hanifa ya kuma sauya yanayin zamantakewa a tsakanain mazauna unguwar Tudun Murtala, ina aka kashe ta, inda har wasu sun fara tunanin tashi daga unguwar.
Tun bayan faruwar lamarin unguwar ta shiga yanayi na firgici da rashin yarda, har a tsakanin makwabata.
A yayin da iyaye suka bayyana kaduwarsu game da abin da ya faru, Aminiya ta samo wasu muhimman bayanai game da mai makarantar da ya yi wa Hanifa kisan gilla daga unuguwar Tudun Murtala.
Tofin Allah tsine kan kisan Hanifa
Jami’an tsaro sun kama Abdulmalik Tanko, mai makarantar Noble Kids Nursery and Primary School da ke Kwanar Dakata, Karamar Hukumar Nasarawa ta Jihar Kano ne kan kisan wata dalibar makaratar mai suna Hanifa Abubakar, mai shekara biyar a duniya.
Abdulmalik Tanko ya sace Hanifa ne daga wani reshen makarantar da ke unguwar Kawaji da ke ’Yankaba a birnin Kano ne a watan Disamba, ya kai ta wata makarantarsa mai suna North West, da ke Tudun Murtala, inda ya kashe yarinyar, ya kuma binne gawarta a harabar makarantar.
Kisan Hanifa dai ta jawo tofin Allah tsine daga mutane daga kowane bangare, ciki har da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da matarsa Aisha da manyan shugabanni da suka bukaci a kwatar wa Hanifa hakkinta a gaban shari’a.
A ranar Litinin ne aka gurfanar da Abdulmalik Tanko da mutanen da ake zargin su tare a gaban kotu, inda kotun ta bayar da umarnin ci gaba da tsare su har zuwa watan Fabrairu.
Kisan Hanifa ya bar baya da kura
Aika-aikar da shugaban makarantar ya yi ta bar baya da kura a unguwar Tudun Murtala inda har yanzu ake ci gaba da zaman dar-dar.
Bayan bullar labarin kisan gillar, a ranar A ranar Juma’a Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin rufewa da kuma soke lasisin makarantar da aka kashe Hanifa aka kuma binne ta.
Kafin wayewar garin Litinin ne wasu matasa suka yi kukan kura suka cinna wa ginin makaratar wuta ta kone kurmus, duk da cewa haya makarantar ta kama ginin.
A yunkurinta na dakile tashin tarzoma bayan harin, Gwamantin Jihar Kano ta soke lasisin daukacin makarantun kudi da ke jihar tare da rufe su.
Wani malamai a unguwar Tudun Murtala ya shaida wa wakilinmu cewa tun kafin karfe 12 na rana, —kimanin awa daya kafin lokacin tashi — iyayen daliba suka yi cincirindo a kofar shiga makarantun kudi domin daukar ’ya’yansu a ranar Talata.
Yawancin makarantun firamari da nazare na kudi da ke Kano suna fara karatu ne karfe 8:00 na safe sannan su tashi karfe 1 na rana.
Iyaye sun bukaci “Izinin shiga”
Aminiya ta gano cewa tuni iyayen dalibai a yankin suka bukaci makarantu su samar da takardun izinin shiga daukar yara domin kar a maimaita irin abin da ya faru da Hanifa.
Wani malami ya shaida mana cewa tun a ranar Litinin wasu iyayen dalibai suka je makaranta suna neman a samar da takardar izinin domin tabbatar da tsaron ’ya’yansu a makaranta.
Ya bayyana cewa makarantun da ke unguwar sun fara yin hakan domin tabbatar da tsaron dalibai da kuma yarda a tsakanin iyayen dalibai da malamai.
Malamai da dalibai na nesa-nesa da juna
Malamin ya ce kisan Hanifa ya haifar da tazara tsakanin malamai da dalibai a yanin, inda suka koma mu’amala nesa-nesa da juna.
Ya ce, “Malamai na tsoron zuwa kusa da dalibai domin gudun zargi, su kuma dalibai suna nisantar malamai saboda tsoron a yi garkuwa da su.”
Zaman zullumi a Tudun Murtala
Duk da cewa an rufe makarantar da aka kashe Hanifa, har yanzu ana zaman zullumi a yankin na Tudun Murtala.
Wata malama a wata makarantar kudi a unguwar ta shaida wa Aminiya cewa makarantu sun ci gaba da karatu, amma har yanzu labarin kisan na daukar hankali a makarantun inda malamai da dalibai suke ci gaba da magana a kai.
Har yanzu akan ga mutanen unguwar sun taru suna tattauna batun, musamman bayan gurfanar malamin da wadanda ake zargin a gaban kotu.
Wani mazaunin unguwar, Yahaya Sa’id, ya ce, “Wannan jarabawa ce ga al’ummar Tudun Murtala, ganin halin dimuwar da aka shiga a kwanan nan saboda lamarin.”
Yahaya Sa’id ya ce, “Muna cikin mawuyacin hali, saboda ba wanda ya san abin da zai biyo bayan kisan. Abin takaici ne saboda yanzu ba wanda ya yarda da hatta makwabcinsa. Kuma ina ganin a haka za a ci gaba zuwa wani lokaci.”
Yiwuwar tashi daga unguwar
Wani dan kasuwa a yankin ya ce sace Hanifa da kuma kashe ta ya jefa al’ummar Tudun Murtala, musamman makwabtan makarantar cikin tashin hankali.
“Abin da ya faru da Hanifa ya jefa daukacin unguwar Tudun Murtala cikin rudani, bisa alama kuma hakan zai iya sa wasu mutanen su tashi daga unguwar.
“Mun yi magana da wasu daga cikin mutanen da ke tunanin tashi su koma wasu unguwannin da zama,” inji shi.
Ya kara da cewa labarin kisan ya taba wasu makarantun da ke unguwar ta yadda wasunsu har yanzu ba su ci gaba da karatu ba.
“Makarantun da ke gasa da Abdulmalik kamar Al-Ibrar da Shajaratul Mubaraka sun dakatar da karatu. Ba a kara ganin mai makarantar ko malamanta ba.
“Watakila kuma su dawo su ci gaba idan abubuwa suka lafa. Amma abin tambaya shi ne ko iyaye za su bari ’ya’yansu su koma makarantun?”
Abdulmalik na da matsalar “Autism”
Dan kasuwar ya ce ya lura da cewa Abdulmalik Tanko na da matsala wajen mu’amala da mutane, ba ya son jama’a.
Ya ce shekara uku ke nan da dawowar Abdulmalik Tudun Murtala da zama bayan ya samu matsala da wani mai makaranata Tudun Wada a karamar Hukumar kan zargin sa da almundahanar Naira miliya biyu.
Amma, “Da kyar yake yin hulda da mutane ko makwabtansa, kullum gidansa a kulle, shi kuma shiru-shiru, sai kuncin rai.
“Bayan sallamar sa a makarantar farko da ya yi aiki a matsayin hedimasta kan zargin cin kudi ne ya dawo Tudun Murtala ya kafa makarantar North West.
“Da likafa ta ci gaba, sai ya kama hayar wani gini a Kwanar Dakata da ke ’Yankaba ya kafa makarantar da ake kira Nobel Kids Academy inda ya yi garkuwa da Hanifa.”
Iyaye na cikin damuwa
Wata mahaifiya a unguwar Tudun Murtala, Fauziyya D. Suleiman, ta ce har yanzu ba ta farfado ba daga irin kidimewar da ta yi saboda samun labarin kisan Hanifa.
Ta ce matsayinta na uwa, abin ya yi mata ciwo sosai kuma za ta dade yana damun ta.
“Neman ilimi dole ne, amma abin da aka yi wa Hanifa ya haifar da mummunan rauni da rashin tabbas a zukatan iyiaye ta yadda yanzu dole su kara yin taka tsansan fiye da kowane lokaci game da wanda za su ba wa amanar ’ya’yansu,” inji ta.
Ta yi kira ga gwamnati da ta dauki matakai tare da tabbatar da wadanda suka cancanta ne kadai take ba wa lasisin bude makarantu.
Shi ma wani mahaifi mai suna Haruna Abubakar ya ce tun bayan bullar labarin kisan Hanifa ya rasa abin da yake masa dadi.
“Sai idan mutum ya sanya kansa a matsayin iyayen Hanifa zai fahimci irin ciwon da abin yake da shi. Na rasa abin da ke min dadi,” a cewarsa.