✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izar matar da IPOB ta kashe da ’ya’yanta a Anambra

An yi jana'izarsu a Anambra bayan da farko an tsara kai su mahaifarsu a Karamar Hukumar Ganye ta Jihar Adamawa domin yi musu jana'iza a…

A safiyar Laraba aka yi jana’izar Harira Jibril, mai cikin da kungiyar IPOB ta yi wa kisan gilla tare da ’ya’yanta hudu da dan cikinta a Jihar Anambra.

An yi jana’izar Malama Harira tare da ’ya’yanta; Fatima, Khadiza, Aziza da Zaituna, wandan IPOB ta kashe su tare a ranar Lahadi ne a garin Awka, babban birnin jihar Anambra.

An yi jana’izar Malama Harira tare da ’ya’yanta; Fatima, Khadiza, Aziza da Zaituna, wandan IPOB ta kashe su tare a ranar Lahadi.

Mijin Harira, Malam Jibrin Ahmed ya shaida wa Aminiya cewa dole ce ta sa aka yi jana’izar iyalan nasa a Jihar Anambra, saboda ba a bai wa gawarwakin kulawar da ta dace ba, har suka fara rubewa a dakin ajiyar gawa.

A cewarsa, hakan ce ta sa ba za a iya yin tafiya da gawarwakin zuwa yankin Arewa ba, duk da cewa ya so ya kai domin a yi masu sutura a mahaifarsu da ke Karamar Hukumar Ganye ta Jihar Adamawa.

Ya ce sai da suka biya Naira 30,000 a dakin ajiyar gawa duk da ba su yi wa gawarwakin komai ba don gudun lakacewarsu.

Haka kuma sai da aka biya kudin daukar gawarwakin Naira 170,000 zuwa inda aka yi masu sutura.

Da yake nasa jawabin, Sarkin Hausawan yankin Orunba ta Kudu a Jihar Anambra, inda aka yi wannan aika-aika, Alhaji Kabiru Bakari ya shaida wa Aminiya cewa an tura Jami’an tsaro suna sintiri, kuma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya ba su tabbacin kula da lafiyarsu da dukiyoyinsu tare da tsare mutuncinsu.

“Sai dai hankalin jama’armu ya tashi muna cikin fargaba kuma ko shakka babu zamu yi kaura mu bar wannan yankin, daman jira muke mu yi wa wadanda aka kashe sutura sannanmu fita mu bar garin,” inji basaraken.

Ya ce an yanke shawarar yi musu jana’iza a Anambra ne saboda gawarwakin ba su samu kulawar da ta dace ba a dakin ajiyar gawa ta yadda za a iya kai su yankin Arewa a yi musu jana’iza a can ba.

“Mun yanke shawarar binne su a Awka ranar Laraba (yau), saboda jami’an dakin ajiyar gawa ba su ba su kulawa da ta dace ba, ba su sanya musu sunadaran adana ba.

“Shi ya sa ba za mu iya tafiya da su ba, domin sun riga sun fara rubewa, yanzu ba mu da wani zabi sai mu binne su a nan Awka,” inji basaraken.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayani kan dalilinsu na jingine shirin kai gawarwakin zuwa mahaifarsu a Jihar Adamawa, domin yi musu jana’iza.

IPOB ta shafe iyalaina a ban kasa —Malam Jibril

Tun da farko, Malam Jibril, magidancin da haramtacciyar kungiyar IPOB ta yi wa iyalan nasa wannan kisan gilla, ya ce yana cikin matukar tashin hankali kuma kungiyar ta shafe iyalansa gaba daya daga ban kasa.

“Yanzu babu wanda ya rage min, sun shafe daukacin iyalina; Ina cikin tsanain tashin hankali, ya kamata gwamnati ta kawo min dauki, ta dauki mataki” inji Jibril.

Malam Jibril, wanda ke aikin gadi a Jihar Anambra, ya ce an yi wa iyalan nasa wannan gisan kiyashi ne a cikin makon da suke sa ran matar tasa, marigayiya Harira za ta haihu.

Magidancin ya yi zargin cewa an kashe Harira da ’ya’yansu hudu ne saboda an gan su sanye da hijabi a lokacin da suke dawowa daga ziyarar da suka kai wa kanwarsa.

Ya ce iyalan nasa da aka kashe sun hada da matarsa Harira Jibril mai shekara  32, sai ’ya’yansu hudu; Fatima mai shekara tara; Khadijah mais hekara bakwai; Aziza mai shekara biyar; sa kuma ’yar autar, Zaituna mai shekara biyu.

A zantawarsu da wakilinmu ta waya a ranar Tatala, Jibril ya ce, “Yanzu haka ina kokarin karbar gwarwakin ne; ’yan sanda sun ba ni takardun da zan je in karbi gawarwakin.

“Yanzu haka ina dakin ajiyar gawa, sun ce sai na biya N30,000 karin su samar min gawarwakin iyalina.

“Ina so in tafi da gawarwakin a binne su a Karamar Hukumar Ganye ta Jihar Adamawa, saboda makabartar da ke nan ta cika.”

Daga baya ne suka sauya shawarar binne mamatan a garin Akwa na Jihar ta Anambra.

’Yan Arewa na shirin kaura daga Anambra

Basaraken ya ce a ranar Talata da yamma ne aka karbo gawarwakin mamatan da aka yi wa kisan gilla a ranar Lahadi.

Sarki Bakari ya ce an girke jami’an tsaro a yankin da abin ya faru kuma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Anambra ya kai musu ziyara tare da ba su tabbacin daukar mataki da kuma kwatar musu hakkinsu.

Ya kara da cewa “Amma idan muka kammala jana’izarsu za mu koma garuruwanmu da ke Arewa, yanzu ba wanda ke cikin aminci daga cikinmu a nan.

“Shi ma mijin matar zai koma Jihar Adamawa da zarar an kammala jana’izar; da ma aikin gadi yake yi a nan,”

Ya ce an girke jami’an tsaro a yankin da abin ya faru kuma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Anambra ya ziyarace su, tare da ba su tabbacin daukar mataki da kuma kwatar musu hakkinsu.

CAN ta la’anci kisan Harira a Anambra

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta yi tir da kisan gillar da aka yi wa Harida da ’ya’yanta, tana mai takaicin abin da ta kira dabbanci da kuma yadda wasu mutane ba su dauki rai a bakin komai ba a Najeriya.

Shugaban CAN na Reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayap, cikin wata sanarwa mai taken ‘Karuwar shaidanci da yin shirun mutanen kirki’, ya koka kan yaduwar miyagun ayyuka da suna addini, yanki, kabila da sauran bambance-bambance a Najeriya.

Don haka kungiyar ta nemi Gwamnatin Tarayya ta kamo duk masu hannu a kisan da aka yi wa wani dan Najeriya da sunan addini ko wani abu.

“Idan gwamnati da hukumomin tsaro ba su tashi tsaye wajen daukar mataki da tabbatar da hukunta masu kisa gilla ba, to ba za a daina irin wannan danyen aiki ba, karshenta ma sai miyagun su hada mu fada da juna, mu kasa ganin laifinsu,” inji Rabaran Hayab.

Matasan Arewa sun yi jan ido

Kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF) ta yi zargin akwai shirin shafe ’yan Arewa mazauna yankin Kudu maso Gabashin Najeriya daga doron kasa a harin na ranar Lahadi.

Shugaban AYCF, Yerima Shettima, ya zargi Gwamnonin Kudu maso Gabas da hannu a kisan ’yan Arewa a yankin, saboda ba sa daukar matakai.

Don haka ya ce gwamnonin Kudu maso Yamma, “Wajibi ne ku kawo karshen yadda ake kashe ’yan Arewa da ba su bi ba, ba su gani ba, ko kuma ku fuskanci hukunci.

“Rashin hana kashe ’yan Arewa barkatai, da gwamnonin Kudu maso Gabas suka kasa a matsayinsu na shugabannin tsaron jihohinsu, ya nuna akwai wata makarkashiya ta shafe ’yan Arewa daga bankasa da sunan harin IPOB ko reshen kungiyar na ESN,” a cewarsa.

Ya kara da cewa ’yan Arewa ba za su lamunci dabi’ar auka wa ’yan uwansu mazauna ko masu gudanar da harkokinsu a yankin Kudu maso Gabas ba, kan abin da kai taka kara ya karya ba.

“Rashin maganar gwamnonin kan kisan gillar da aka yi wa ’yan uwanmu maza da mata a Kudu, dole ne a daina.

“Muna kuma jan kunne cewa babu wani dan Najeriya da ya fi wani iya rikici, saboda haka kada a yi kuskuren daukar yadda ’yan Arewa ke bin doka a matsayin kasawa.”

Tun ranar Lahadi wannan lamari ya faru, amma manyan kafofin yada labarai ba su dauka ba, duk kuwa da yadda hotunan suka karade kafofin sada zumunta.

Aminiya ta bibiyi lamarin kisan gillan, wanda kungiyoyi da sauran masu rajin kare hakkin dan Adam da hukumomin tsaro sun yi tir da abin da suka kira munafincin manyan kafofin yada labarai, musamman na yankin Kudu, kan rashin daukar labarin.

Ba ’yan Arewa kadai ake kai wa hari ba —Soludo

Amma a jawabinsa kan harin, Gwamnan Charles Soludo ya musanta zargin kai hare-hare na musamman a kan ’yan Arewa a jiharsa, yana mai bayyana cewa babu wani bangare da ya tsira a matsalar da  addabi jihar.

A cewarsa, maharan sun fi kashe ’yan asalin jihar fiye da sauran mazauna jihar a hare-haren kungiyar.

Sanarwar da kakakinsa, Christian Aburime, ya fitar ta ce labarin da ake cewa ’yan Arewa ake kai wa hari na iya tayar da rikici a Najeriya.

Soludo ya ce, “Gaskiya ne ana fama da matsalar tsaro a fadin Najeriya, amma babu wata kabila ko addini da ake warewa kai mata hari a Jihar Anambra.

“Hasali ma ’yan asalin jihar sun fi kowa yin asarar rayuwa a sanadiyyar ayyukan masu kashe-kashen; saboda haka rahoton bai dace ba, yana kuma iya raba kan kasar nan.

“Gwamnatin Jihar Anambra na zargin an sanya ra’ayi cikin rahoton don haka ya kamata a janye shi, a bayyana ainihin abin da ya faru.”

Ya jaddada cewa ’yan asalin jihar da ’yan Arewa da sauran mazauna jihar sun dade suna zaune da juna lafiya suna gudanar da harkokinsu cikin aminci ba tare da wata matsala ba.

Don haka ya yi alkawarin ci gaba da kokarin tabbattar ayyuka nagari domin cigaban duk al’ummar jihar.

’Yan sanda sun ba wa Hausawa tabbacin kariya

A ranar Talata, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Anambra, Echeng E. Echeng, ya ba wa al’ummar Hausawa da ke zaune a jihar tabbacin samun cikakkiyar kariya.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce an fara gudanar da binciken lamarin, kuma an girke jami’ai a muhimman wurare domin tabbatar da tsaro a sassan jihar.