Kimanin mako biyu ke nan da aka samu labarin yadda wadansu da ake zargin makiyaya ne sun kai mummunan hari a kananan hukumomin Dekina da Omala da ke Jihar Kogi.
A harin, an kashe akalla mutum 32 ne ciki har da wani Basarake Musa Edibo, wato Onu Agbenema, tare da matarsa.
Sauran kauyukan da harin ya shafa sun hada da Abejukolo da Obakume da Idirisu da Oji Apata Agbenema da Al’ichekpa da Opada da kuma Iyade.
Kisan ya auku ne makonni kadan da Gwamnan Jihar Alhaji Yahaya Bello ya ce ya samar wa makikaya hekta dubu 15 na filin yin kiwo. Gaskiya yunkurin da Gwamnan ya yi na samar da wannan fili ya cancanci yabo don yunkuri ne da zai iya kawo karshen fadace-fadacen da ke faruwa a tsakanin manoma da makiyaya a jihar, amma abin mamaki duk da haka sai aka ci gaba da samun tashin hankali.
Don haka muna Allah wadai da wannan harin da aka kai, kuma muna kira ga Gwamnatin Jihar da ta Tarayya da jami’an tsaro da su yi kwakkwaran bincike don zakulo wadanda suka yi wannan aika-aika don su fuskanci hukunci mai tsanani.
Shirin da rundunar soji ta kaddamar a yankin mai taken Operation Cat Race bai yi tasiri ba ke nan, tunda an ci gaba da kai munanan hare-hare. Hakan ya nuna akwai bukatar rundunar sojin ta sake taku.
Rahoton ya nuna yadda ’yan ta’addan suka yi amfani da karfi wajen mamaye kauyukan ta hanyar sanya shingayen da ba shiga ba fita kuma suka ci karensu babu babbaka, duk da cewa akwai rundunonin tsaro a yankin.
’Yan ta’addan sun kashe na kashewa, suka kona gidaje, suka wawure dukiya mai dimbin yawa yayin da sauran jama’ar da suka yi sa’a suka ranta a cikin na-kare don tsira da rayukansu.
Don haka muna kira ga jami’an sojin da ke da alhakin kula da yankin su canja taku, domin da alama shirin samar da zaman lafiya mai taken: Operation Cat Race bai yi wani tasiri a yankin ba.
Sannan kisan da aka yi a Kogi ta Gabas ya nuna har yanzu akwai matsala game da yunkurin da Gwamnatin Tarayya take yi na samar da tsaro a sassan kasar nan. Abin takaicin ma shi ne yadda al’ummar da ke zaune a karkara suka fi fuskantar matsalar tsaro, inda ba kasafai ake ganin jami’an tsaro a yankunan don kare lafiyarsu da ta dukiyoyinsu ba. Kuma abin bakin ciki ne yadda aka kasa samar da jami’an tsaro na sirri (SSS) da za su rika tattara bayanan sirri musamman a kauyuka da hakan zai ba da damar sanin hanyoyin da suka kamata a bi don a rika dakile aukuwar kai hare-hare.
Don haka muna kira ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta yi kokarin samar da abubuwan bukatun rayuwa da suka hada da abinci da magunguna da suturu da sauransu ga ’yan gudun hijirar Kogi ta Gabas.
Sannan akwai bukatar Asusun Tallafawa Wadanda Bala’i Ya Shafa (bSF) ya kai ziyarar gani da ido yankin, don tantance irin asarar rayuka da ta dukiyoyi da aka yi, daga nan ya tallafa wa al’ummar da bala’in ya shafa don su ci gaba da gudanar da rayuwa mai inganci.
Yanzu dai al’amarin fada a tsakanin manoma da makiyaya ya dauki sabon salo, inda a kullum za ka ji suna sukar juna da fada wa juna bakaken maganganu da hakan ke tayar da fitina.
Ba za a taba samun ci gaba a duk wurin da babu kwanciyar hankali ba don haka muna kira ga shugabanni musamman masu rike da mukaman siyasa su yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen tashe-tashen hankulan da ke faruwa a sassan kasar nan.
Ga dukan alamu, babu wata kabila da ke murna da yadda ake yawan samun tashin hankali walau a bangaren manoma ko na makiyaya.
Ya kamata gwamnati ta yi hobbasa wajen ganin ta kawo karshen yawan fadace-fadacen da ke faruwa a tsakanin manoma da makiya a kasar nan. Ya dace ta yi kokarin ganin ta hada kansu wajen zama lafiya don a samu ci gaba mai ma’ana.
Lokaci ya yi da za a zakulo ’yan ta’addan da suka addabi sassan kasar nan Kudu da Arewa don a hukunta su domin hakan zai samar da zaman lafiya mai dorewa.