Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta yi watsi da ratoton Majalisar Dinkin Duniya (MDD) mai cewa manoma 110 ne mayakan Boko Haram suka kashe a Zabarmari, Jihar Borno.
A ranar Lahahi, Ofishin MDD na Najeriya, ta bakin Babban Jami’insa, David Kallon, ya ce bayan mutum 43 da aka binne a ranar, an gano ragowara gawarwaki a warwatse wanda hakan ya kai adadin ga 110.
- Yadda ’yan Najeriya suka fusata da kisan manoma a Borno
- Manoma 110 ne aka kashe a Zabarmari —MDD
- Budurwa ta yi wa mahaifiyarta gunduwa-gunduwa
Amma safiyar Litinin, kakakin Hedikwatar Tsaron, Manjo Janar John Enenche ya yi watsi da rahoton inda ya ce manoman shinkafa 43 ne mayakan suka kashe sabanin rahoton na MDD.
Enenche wanda ya kasance bako a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels ya ce sojoji tare da mazauna ne suka tattara tare da kirga gawarwakin kuma 43 suka samu ba 110 ba.
Aminiya ta kawo muku rahoto, inda ta ambato Kallon na cea mutum 110 ne aka kashe, lamarin da ya kai ga sabunta kiraye-kirayen a kori Manyan Hafsoshin Tsaro.
Sai dai Enenche ya shaida wa shirin cewa ya tuntubin kwamandojin rundunar da ke bakin daga don jin hakikanin abin da ke faruwa, sannan ya ce ana ci gaba da neman ko akwai karin mamata.
“Na san hakan za ta taso musamman saboda maganar ta fito ne daga MDD ba wata majiyar da ba ta son a ambaci sunanta ba. Wannan sanannkiyar majiya ce ta ce mutum 110 aka kashe.
“Sun ba ni talhisin abin da ya faru. Kafin zuwan gwamnan wajen bayan lamarin sai da sojoji suka kirga gawarwakin suka samu 43. Tabbas wasu sun tsere sun shiga dazuka amma sun fara dawowa.
“Da misalin karfe biyu jiya (Lahadi), na kira su, zuwa karfe 7 ba dare sun tuntube ni cewa suna sake kirgawa suna kuma kara nema ko za su samu karin gawarwarki.
“Ba lallai ne mu samu adadin da shi (Kallon) ya bayar ba, amma zuwa yanzu mutum 43 muka gano tare da mazauna, muna kuma fata kar adadin ya karu.
“Halin da ake ciki ke nan. Ba barci muka yi ba, muna ci gaba da bibiyar lamarin musamman kasancewar bayanin ya fito ne daga Majalisar Dinkin Duniya”, inji shi.