Kotu ta yanke hukuncin dauri a kan sojojin da ke tsaron tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya Alex Badeh.
Hukuncin kotun ya biyo bayan kisan Air Marsha Alex Badeh da ‘yan bindiga suka bude wa wuta a hanyarsa ta dawowa daga gona.
Kakin Rundunar Sojin Saman Najeriya Air Commodore Ibikunle Daramola ya ce kotun sojin saman ya yanke hukuncin ne a kan sojoji shida.
Hudu daga cikinsu su masu kare lafiyar tsohon Babban Hafsan ne. Sauran biyun kuma masu gadi ne a gidansa.
Sanarwar da ya fitar ba ta ambaci adadin shekarun da ta yanke wa kowanne daga cikin sojoin ba.
Shugaba kotun Air Commodore David Aluku ya ce sojojin sun aikata laifukan da ake tuhumarsu.
Laifukan sun hada da kin ba wa Alex Badeh kariya da kuma sulalewa daga ayarin motocinsa sadda aka kai masa hari.
Sauran sun hada da bayar da bayanen kanzon kurege da sakaci da kuma saba ka’idar aikin soji.
Lauya wadanda ake zargin ya nemi kotun ta yi sassauci kasancewar wannan ne karon farko da suka aikata laifi.
Hukuncin zai tabbata ne idan kotun gaba da wannan kotun ta amince da shi.
Bayan an kashe Alex Badeh ne jami’an tsaro suka kama wasu mutane a kan titin Gitata-Keffi da abin ya faru.
Mutum 14 da ake zargin sun yi wa jami’an tsaron ikirarin cewa su ‘yan fashi ne akan titin.