Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), a Jihar Kano ta tura ma’aikata 1,539 domin tabbatar da tsaron hanyoyi da zirga-zirgar ababen hawa a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na FRSC, Abdullahi Labaran, ya fitar.
Kwamandan hukumar a jihar, Umar Matazu, ya ce manufar aikin ita ce rage yawan haɗura da kuma kare rayuka da dukiyoyin mutane a kan hanyoyin Kano a lokacin bukukuwan.
Hukumar ta tura motoci 25 na sintiri, motoci guda biyar na ɗaukar marasa lafiya, babbar motar jan manyan motocin da suka lalace, da kuma sauran kayan aiki.
Aikin nasu ya karkata ne a kan manyan hanyoyi guda shida a jihar.
Matazu, ya jaddada muhimmancin bin dokokin hanya ga direbobi, guje wa tuƙin ganganci da wuce gona da iri, tare da kiyaye lafiyar kowa da kowa.
Ya kuma bayar da shawarar cewa direbobi su tsara tafiyarsu a kan lokaci, su guji tuƙin dare, sannan su kira lambar gaggawa ta FRSC 122 idan akwai wata matsala ko su je ofishin FRSC mafi kusa don samun taimako.
Har ila yau, ya buƙaci haɗin gwiwar jama’a da hukumar don tabbatar da bukukuwan Kirsimeti ba tare da haɗura ba.
Ya ce, “Mu yi aiki tare domin tabbatar da cewa bukukuwan bana sun gudana lafiya.
“Ina muku fatan yin bikin Kirsimeti mai albarka da sabuwar shekara cikin aminci.”
Hukumar ta tabbatar wa da jama’a cewa ta shirya tsaf domin tabbatar da tsaron hanya da rage yawan haɗura a lokacin bukukuwan da bayan su.