✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kirsimeti: CAN ta shawarci ’yan Najeriya su yi taka-tsan-tsan

Shugaban CAN na kasa ya yi fatan kawo karshen ta’addaci a Najeriya.

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta shawarci ’yan kasar, musamman Kiristoci su sanya ido sosai tare da yin taka-tsan-tsan yayin shagulgulan Kirsimetin bana saboda yanayin tsaro.

Shugaban CAN na Kasa, Dakta Samson Ayokunle ne ya bayyana hakan cikin sakonsa Kirsimeti ga mabiya addinin a ranar Alhamis.

A cewarsa, “A yayin da muke murnar bikin Kirsimeti, ya kamata mu sa idanu sosai a kan harkar tsaro, sannan mu kiyaye matakan kariya daga cutar COVID-19.”

Ya ce bikin Kirsimeti ba al’ada ba ce, ko wani biki kawai, lokaci ne da kowa ya kamata ya kasance cikin farin ciki.

Dakta Samson ya kuma yi kira ga Kiristocin Najeriya kan su yi amfani da bikin wajen fadakar da al’umma kan abin da ya shafi garkuwa da mutane, fashi da makami, yaki da sauran tashe-tashen hankula da a halin yanzu suke addabar kasa.

Sai dai ya ce hakika bikin na bana ba zai yi wa wasu dadi ba saboda rashin ’yan uwansu da suka yi a sanadiyyar cutar COVID-19 da kuma ayyukan ’yan ta’adda.

Daga nan shugaban na CAN ya yi addu’ar gwamnati ta samu damar kawo karshen matsalar tsaro baki daya a Najeriya, tare da fatan ganin karshen cutar COVID-19 baki daya a duniya.