Tun a cikin watan Yunin 2012, kungiyar Gwamnonin jihohin kasar nan 36, a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Ribas na wancan lokacin, yanzu kuma Minsta Sufuri Cif Rotimi Amaechi, ta yi kiran lallai a bar jihohi su kirkiro `yan sandan jihohinsu. Babban hanzarin da kungiyar ta bayar a wancan lokacin, babban hanzarin da suka bayar don samun biyan bukata shi ne matakan tsaron kasar nan na kara sukurkucewa. Amma kafin `yan kasa su gama fahimtar fa`idojin waccan bukata sai kungiyar gwamnonin jihohin Arewa 19, in ban da Gwamnan Jihar Filato a cikin watan Yulin 2012, suka ba da shelar janyewarsu daga neman a kirkiro masu `yan sandan jihohin.
Bayan janyewar gwamnonin jihohin Arewar sai kuma ga shi a cikin watan Agustar 2012, Sufeto Janar na wancan lokacin, bayan wata ganawa da ya yi da Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan a fadar shugaban kasa Abuja, ya bayyana wa manema labarai kiyayyarsa a kan jihohi su kafa rundunonin `yan sandan jihohi, al`amarin da ya ce `yan siyasa kawai za su rinka amfani da `yan sandan don biyan bukatunsu. Hakazalika, wakilai a taron nema wa kasar nan makomar siyasa na shekarar 2014, da Gwamnatin Shugaba Jonathan ta gudanar, daya daga cikin kudurorin da suka zartar, har da batun neman a kirkiro rundunoni `yan sandan jihohi.
Shi kansa Mukaddashin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a cikin watan Yulin 2016, an ji shi yana kiran lallai lokaci ya yi da jihohi za su samu rundunonin `yan sanda na kashin kansu, yana mai jaddada cewa lokacin da yake Kwamishinan shari`a na Jihar Legas, sau 10, yana tunkarar Kotun koli a kan batun a kirkiro `yan sandan jihohin. Shi ma tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Ibrahim Babangida a watan Yunin da ya gabata, an ruwaito shi yana nuna goyon bayansa akan lallai yanzu lokaci ya yi da za a bari jihohi su kafa `yan sandan jihohinsu, yana, mai watsi da fargabar da ake da shi na zargin gwamnonin jihohin za su rinka amfani da su don biyan bukatun kansu.
Tun dai a cikin watan Satumbar bara dan Majalisar Wakilai Awoleye Abiodun ya gabatar wa Majalisar daftarin dokar neman a kafa rundunonin `yan sandan jihohi, bayan an gyara sashe na 214 na kundin tsarin mulkin kasar nan da yanzu ake kokarin sake yi masa kwaskwarima, sashen da shi ya yi tanadin kafa Rundunar `yan sanda ta kasa daya kilo, kuma ya dora ikon tafiyar da ita a hannun gwamnatin tarayya.
Duk kuwa da Majalisar Wakilan a ranar 27 ga watan na Satumbar bara ta yi wa daftarin dokar neman kafa `yan sandan jihohin, amma tabbataccen rahotan da ake da shi yanzu shi ne Kwamitin hadin gwiwa don gyaran Kundin tsarin mulkin kasar nan da Majalisun Dokokin suka kafa a karkashin jagorancin Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweremadu, ya yi wurgi da wancan daftarin na Wakili Abiodun da yake neman a kirkiro `yan sandan jihohin. Kwamitin hadi gwiwar Majalisun Dokokin na gyaran kundin tsarin mulkin kasar nan da ya kammala aikinsa a Legas a cikin watan Yulin nan da ya gabata an ce ya yi watsi da waccan daftari na bukatar a kafa `yan sandan jihohi, kasancewar batun ba ya cikin irin batutuwan gyaran kundin tsarin mulkin da aka gabatar masa tun farko.
Ana cikin irin wannan danbarwar, sai ga shi a ranar Alhamis 20 ga watan Yuli lokacin da ya gabata, bayan wani taro da ta yi da Sufeto Janar din `yan sandan kasar nan Alhaji Ibrahim Idris a fadar shugaban kasa kungiyar gwamnonin jihohin kasar nan 36, sun sake gabatar masa da bukatar lallai ya sanar da Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo bukatar a sahale masu su kirkiro Rundunonin `yan sanda na jihohinsu. Tatsunniyar gizo dai ba ta wuce koki, hanzarin da kungiyar gwamnonin ta gabatar a 2012, shi ta sake gabatarwa ma a yanzu, wato, tabarbarewar matakan tsaro, da ta ce sun kara ta`azzara.
Don kungiyar gwamnonin jihohin ta nuna da gaske take a kan neman wannan bukata ta sanya zuwa yanzu ta kafa wani Kwamiti da ya kunshi gwamnonin jihohin Imo da Bauchi da Delta da Sakkwato da Ekiti da Kwara, wato gwamna daya daga kowace shiyya shidda ta kasar nan, da ta dora wa alhakin tabbatar da wanzuwar hakan, don ganin ingantuwar matakan tsaro.
Kodayake a wajen taro Sufeto Janar din bai nuna wa gwamnonin adawarsa da kafa rundunonin `yan sandar mallakar gwamnatocin jihohi, amma daga bisani ya sa an fitar da wata sanarwa da take jirwaye mai kamar wanka a kan nuna adawarsa da samuwar hakan, kamar yadda takwaransa na lokacin Shugaba Jonathan ya nuna.
Ko shakka babu dukkan sassan kasar nan suna fama da irin tasu annobar ta sukurkucewar matakan tsaro, kama daga sacewa da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da ta game kasa zuwa fashi da makami da rikice-rikice masu kama da kabilanci ko addini da rigingimun Fulani makiyaya da manoma da sace garaken shanu da annobar fyade da ita ma ta game kasa da ta`addancin `yan daba da na sara suka da na `yan kalare, baya ga masu fasa bututun man fetur a yankin Neja Delta da sauran miyagun ayyuka da ake ta aikatawa ba kaidi ko’ina a cikin kasa.
Da irin wadannan miyagun ayyuka da ake aikatawa mai karatu ka iya cewa lallai lokaci ya yi da jihohi za su samu `yan sandan kansu da za su rinka bi masu kaidin irin miyagun laifuffukan da ake ta yawan aikatawa sasakai. Amma abin tambaya a nan shi ne anya kuwa samar da `yan sandan jihohin da ake ta fargabar gwamnonin ka iya mayar da su karnukan farautarsu wajen kuntatawa tare da gallaza wa abokan hamayyarsu, zai kawo karshen miyagun laifuffukan da ake aikatawar, miyagun laifuffukan da akasari ake aikatasu da daurin gindin wasu gwamnonin jihohin da wasu makarrabansu ko sauran masu rike da madafun iko a kasar nan? Amsa bisa ga ra`ayina ita ce zai yi matukar wahala.
Idan gwamnonin jihohi na tutiyar cewa `yan asalin jihohinsu za su dauka da suka san lungu da sakon birane da karkararsu aikin dan sandan, ai tuni Rundunar `yan sanda ta kasa take tafiyar da tsarin ajiye akasarin manya da kananan `yan sandanta a kusan garuruwansu ko jihohi ko ma a shiyoyinsu na haihuwa, amma ta`asar ta gagara shawo wa.
Kowa ya sa ni musamman gwamnonin jihohi cewa `yan sandan kasar nan na fama da matsalolin da dama, kama daga karancinsu zuwa rashin horarwa da uwa uba kudin da za su tafiyar da ayyukansu na yau da kullum. Gwamnonin jihohin sun kwan da sanin da a yau za su ce ba su kara taimaka wa rundunonin `yan sanda da ke jihohinsu, haka su ma shugabannin majalisun kananan hukumomin kasar nan su ce haka, to kuwa aikata ta`asar sai ta wuce a ba da labari.
Ya kamata dai gwamnonin su sake nazari, su kuma `yan sanda su yi kokarin gyara miyagun halayensu munana su rinka gudanar da ayyukansu cikin kamanta gaskiya da adalci, ta haka kawai nike ganin matakan tsaro za su inganta, amma ba ta kafa `yan sandan jihohi ba. Lokaci ya yi da za mu daina neman aiwatar da tsarin da kasashen da suka ci gaba suke da shi, don kawai muna tafiyar da mulkin dimokuradiyya.