A wani bangare na inganta dangantaka tsakanin addinai, wasu Kiristoci sun taya Musulmai share filin Idi a garin Kachiya da ke Jihar Kaduna, a karshen mako.
Mutanen, wadanda suka hada da matasa da dattijai maza da mata dai sun yi fitar dango ne domin nome ciyayin da suka yi girma sosai a filin sakamakon daminar da ake ciki.
- Hajjin bana: Tukari sun mamaye masaukan alhazan Najeriya a Mina
- Gwamnan Kano ya raba wa Kwamishinoninsa 19 ma’aikatu
Sakataren Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), reshen Karamar Hukumar Kachiya, Mallam Ibrahim Tasiu, ya bayyana jin dadinsa da yadda Musulamai da Kiristocin suka fita aikin sosai.
Ya kuma yaba wa kokarin Kwamitin Tabbatar da Zaman Lafiya a Tsakanin Addinai (IMC) da Hukumar Tabbatar da Zaman Lafiya ta Jihar Kaduna (KAPECOM) da tawagar Mercy Corps kan irin rawar da suke takawa wajen bunkasa zaman lafiya.
Shi ma Ko’odinetan kungiyar ta IMC a Jihar Kaduna, Samso Auta, ya taya Musulmai murnar Sallah Babba, inda ya yi musu fatan yin shagulgula lafiya.